ZA KAYI ƊARURUWAN SHEKARU A ƘABARI



ZA KAYI ƊARURUWAN SHEKARU A ƘABARI.
-
"Zaka kwashi ɗaruruwan shekaru acikin ƙabarinka kai kaɗai daga kai sai aikinka, babu koda mai kawo maka ziyara daga nan duniya, aikinka ne kaɗai zai zama makwancin ka, mai kyau ne shi ko mara kyau, babu damar jin labarin abinda ka bari a duniya daga gurin danginka addu'arsu kaɗai da aiyukan alkhairan da suka yi domin ka ne kaɗai zai riskeka"
-
"Mala'iku babu ruwansu da yawan abinda kake dashi a wannan duniyar, babu mai damuwa da kuɗinka, ƴa'ƴanka, iyalanka, wacce iriyar mota kake tuƙawa, wane irin gida kake rayuwa acikinsa, kawai abinda zai zama abinda dubawa shine kaɗai aiyukan ka"
-
"Idan ka zamto daga cikin masu fifita lahirarsu fiyeda duniyarsu, ka zamto mai kyautata aiyukan ka, mai yawan biyayya ga Allah maɗaukakin sarki da kuma Manzonsa, ka guji zaluntar bayin Allah, to sai kaga ka wanye lafiya a ranar ƙiyamah, ranar da ake fito da mutane daga cikin ƙabarinsu domin ayi musu hisabin aiyukan su na wannan duniyar"

________________
👉🏽Yaku 'yan'uwa masu albarka ku kasance da Da'awa Fisabilillah domin ilimintarwa, fadakarwa tare da tunatarwa.
 
👉🏽Biyomu Facebook
https://www.facebook.com/DaawaFisabilillah/

👉🏽Biyomu Telegram
https://t.me/DAAWAFISABILILLAH

👉🏽Biyomu Youtube
https://youtube.com/channel/UCQezh3JEjj6gfvCv6GLZIDA

Dan uwanku a musulunci
      ABU--MUS'AB ✍️
      ABU--UNAISA ✍️
Post a Comment (0)