RAMADANIYYAT



Ramadaniyyat 1442H [1]

Annabi (SAW) Da Al'ummarsa: Tsananin Bukata Da Gagarumar Nasara:

1. Allah SWT ya yi wa wannan al’umma baiwar aiko mata da fiyayyen annabawa, a daidai lokacin da al’ummar Larabawa da sauran al'umman duniya suke cikin fagamniya da dimuwa da rashin sanin makama da alkibla, kamar yadda Allah SWT ya bayyana hakan a cikin [Suratul Ali Imran 164 da Suratul Jumu’a: 2] 
2. Dan'adam ya kasance yana rayuwa a cikin bata mabayyani, duk da cewa kafin a aiko Annabi (ﷺ) akwai sauran burbushin addinin Yahudu da na Nasara da addinin Annabi Ibrahim (AS), sai dai kuma duk an canja su an jirkita su.
3. Annabi (ﷺ) ya zo da shiriya wadda ta haskaka zukata, ya fitar da al'ummar Larabawa daga cikin duhun jahilci, ya ‘yanta su daga zaluncin azzalumai, wadanda suka kasance suna umartar su da sabon Allah, suna kuma nuna musu bin son zuciya a cikin dukkanin sha’anin rayuwarsu. Annabi (SAW) ya fitar da mutane daga kuncin duniya zuwa yalwarta, daga zaluncin addinai zuwa ga adalcin Musulunci.
4. Hakanan Annabi (ﷺ) ya samu nasara kan abin da ya zo da shi na tabbatar da bautar Allah SWT shi kadai, da nuna cewa bautar wanin Allah aikin banza ne, ba zai amfanar da mai yin sa da komai ba. 
5. Hakanan Annabi (ﷺ) ya ci nasara wajen samar da wata al’umma da ta dauki nauyin isar da sakon da ya zo da shi, wanda haskensa ya shiga ko’ina da ina. Annabi (ﷺ) ya fitar da al’umma daga zalunci da munanan dabi’u da suka hada da mugunta da ganin kyashi da jiji da kai da nuna isa.
6. Hakanan Annabi (ﷺ) ya yi nasara wajen koyar da zamantakewar iyali, watau mutum ya san yadda zai iya gyara gidansa, tun daga kan matarsa da ‘ya’yansa da jikokinsa da duk sauran wadanda suke karkashinsa, ya dora su a kan hanyoyin rabauta da samun dacewa a duniyarsu da lahirarsu.
7. Annabi (ﷺ) ya ci nasara wajen nuna wa mutum yadda zai yi mu’amala da wadanda yake rayuwa tare da su; yadda zai yi mu’amala da iyayensa da makotansa. Ya nuna masa yadda zai yi kyakkyawar mu’amala a kasuwancinsa, ko shugabancinsa. Ya koyar da yadda zai yi mu’amala da dabbobin da ke kewaye da shi, wadanda Allah SWT ya hore masa su don amfanin kansa? 
8. Duk wani abu da Allah SWT ya halitta, a sama yake ko a bayan kasa, shiriyar Annabi (ﷺ) ta riske shi. Wannan shiriya ita ce shiriyar Alkur’anin da ya zo da shi, ya nuna wa dan’adam yadda zai sarrafa wadannan al’amura, da yadda za su zama masu amfani a gare shi, ba yadda zai yi amfani da su ya cutar da kansa ko ya cutar da waninsa ba.
9. Don haka bukatar dan'adam zuwa ga sakon Annabi (SAW) bukata ce ta dole, ba zai iya kauce mata ba, don rayuwarsa ta yi kyau. 
10. Shi kuma Manzo (SAW) da Allah ya dora wa wannan alhaki ya yi samu gagarumar nasara a cikin rayuwarsa da bayan komawarsa zuwa ga Allah. Mun shaida da haka mun yi imani ba ma kokwanto a kan haka ko kadan.
Allah ya raya mu a kan shiriyarsa ya kuma tashe mu a karkashin tutatarsa (SAW).


https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)