DUNIYAR ALJANU DA SHAIƊANU 16


*🌎DUNIYAR ALJANU DA SHAIDANU 16🌎*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
⌨09032091131
+237665087032
.
.
.
Yau 04/ 03/ 1441 wanda yayi dai dai da 01/ 11/ 2019. Cigaba da lekca mai taken *DUNIYAR ALJANI DA SHAIDANU*
=
Wannan shine bayani na goma sha-shida
=
=
*ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻟِﻠَّﻪِ ﻧَﺤْﻤَﺪُﻩُ ﻭَﻧَﺴْﺘَﻌِﻴﻨُﻪُ ﻣَﻦْ ﻳَﻬْﺪِﻩِ ﺍﻟﻠﻪُ ﻓَﻠَﺎ ﻣُﻀِﻞَّ ﻟَﻪُ، ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﻀْﻠِﻞْ ﻓَﻠَﺎ ﻫَﺎﺩِﻱَ ﻟَﻪُ ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻟَﺎ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ ﻭَﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ*
_Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin sarki, Tsira da aminci Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad s.a.w da alayensa da sahabbansa baki daya._

_Bayan haka jama'a wannan zauren *MAJALIS SUNNAH* masu albarka da mutunci barkanku da wannan lokacin._

_Bayan haka! Jama'a mukace idan da gaske an halicci aljani da wuta, tho yaya kuma za ayi ranar kiyama ayi musu azaba da ita?? Amsa:- Eh babu shakka aljani an halicce su ne da wuta amma nan ana gayamaka asalin abune da aka halicce sune, daga baya halittar su ta koma nauyi daban daban. Wasu aljanin sun koma iska, wato yadda kaga iska. Tho haka aljanin wasu suke, wasu aljanin sun koma karnika ne, wasu macizai, wasu kuma kunnamai ne. Da fatan kungane?? Kamar yadda kai dan Adam aka halicci babanka da kasa, amma kuma kai ba da kasa akayi ka ba, saboda ba kasa aka diba aka kwabe akayi ka ba. A'a maniyyi ne daga kwankwason mahaifinka ya gangaro ya taho azzakari, yazo ya gangaro ya shiga farji, daga nan sai Allah ya sauwaraka sai ka zama mutum. Kaga ashe asalin halittar Adamu da kasa ce, amma sai halittar dan Adamu ta koma da maniyyi, Don haka sai dan Adam ya fito a soka da nama da keshi da bargo da kuma fata. Kungane??_

_Tho tambaya anan shine idan aka dauki kasa aka kwada maka zakaji zafi ko bazaka ji ba?? Amsa:- Zakaji zafi, tho amma ai kaga da ita akayi ka amma kuma gashi zatayi maka rauni. Tho haka shaidanu da aljani ma za a azabtar dashi da wuta. Kungane amsar da kyau ko?? Tho idan kungane da kyau sai mu shiga tambaya ta gaba, shin yaya shakalin aljani yake?? Ma'ana kamar yadda na mukace wasu aljanin suna nan a iska ne. Tho amma kuskuren da mutane suke tunani shine duk inda akace aljani, tho sai kaji ance iska ne. Gaskiya kuskure ne wannan. Tho mu yanzu duk inda kace mutum, tho nama ne da tsoka da bargo da keshi da fata da kuma gashi. Kunga wadannan sune suka hadu suka zama mutum ko? Tho amma aljani ba haka bane, wasu aljanin iska ne, iska sak amma kuma aljani ne da ranshi, wani aljanin tun farko da Allah yai shi maciji ne amma kuma aljani ne. Wani aljanin kuma Allah ya ishi kare. Sai Annabi Muhammad s.a.w yace "Duk inda kaga bakin kare tho Shaidani ne, tho yanzu bakin kare kare ne a kare, amma kuma aljani ne, a aljanin ma Shaidanu. Kunga ashe akwai aljanin da Allah ya ishi a matsayin kare kenan ko? Tho Manzon Allah s.a.w acikin wani hadisi wanda ya bayyana wa sahabbansa cewa akwai wasu dabbobi da Allah madaukakin sarki ya shafesu, da ya shafesu ya zam aljani, sai suka koma sai suka zama macizai. Tho anan ba dukkan maciji ba fah ake nufi. Misali kamar yadda akwai wasu yahudawa da suka taba yiwa Allah laifi, yace kada suyi kaza, tho sai sukayi ranar asabar, da sukayi suna ganin sunyi dabara, tho da Allah madaukaki sarki ya tashi sai ya mayar da su birai, wasu kuma Allah ya mayar dasu aladai. Tho yanzu wannan maganar ba cewa akayi duk inda kaga birai kace ai bayahude ne ko duk inda kaga aladai. A'a akwai wasu birai dai da ya zam asalinsu mutane ne Allah ya mayar dasu haka. Akwai wasu aladai asalinsu mutane ne Allah ya mayar dasu haka, amma fah basu kai labari ba, saboda da Allah ya mayar dasu wadannan dabbobin sai ya hallaka su. Ma'ana yanzu babu labarinsu kenan. Don haka duk inda kaga biri, tho biri ne. Duk inda kaga alade, tho alade ne ba bayahude bane. Da fatan kungane?_

_Tho sai Annabi s.a.w yake cewa akwai macizan da aljanu ne aka taba shafesu suka zamo macizai, kamar yadda aka taba shafe wasu Bani Isra'il suka zama alade da birai. {Ibn Hibban ne ya rawaito shi da shi da Dabarani da Ibn Hakim. Hadisi ne sahihi. Abinda yasa muka kawo wannan hadisi shine don ka iya bambance yadda al'amarin yake saboda karku rikice, don kaga anayi maka bayanin wata duniya ne wanda mutane sun ta fassara ta da kuskure._
.
=
=
Zamu dakata anan sai bayani na gaba Inshaa Allahu.
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)