MU KULA DA ADDININ MU 01


*(((💌 MU KULA DA ADDININ MU🌸)))*

      *JAN HANKALI NA DAYA (1)*

Da azumi ya kama sai kaji 'yanmata suna cewa 'Don Allah mallam ataya mu da addu'a Allah ya bamu miji na gari'.

Sai dai fa da zaka kalle rayuwar wacce tace ataya ta da addu'an, mafi yawancin rayuwar ta bata damu da addini ba. Ita ce:

1. Rashin kula da sallah.

2. Bayyanar da tsiraici (fita ba tare da irin suturar musulunci ba).

3. Jin wakoki. Da sauran su. 

Yar'uwa anya kin dace da namiji na gari kuwa ? Domin Allah madaukakin sarki yana cewa:

(الخَبيثاتُ لِلخَبيثينَ وَالخَبيثونَ لِلخَبيثاتِ ۖ وَالطَّيِّباتُ لِلطَّيِّبينَ وَالطَّيِّبونَ لِلطَّيِّباتِ ۚ أُولٰئِكَ مُبَرَّءونَ مِمّا يَقولونَ ۖ لَهُم مَغفِرَةٌ وَرِزقٌ كَريم).ٌ (سورة النور :٢٦).



                   *Alhanafee*
Post a Comment (0)