*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 07```
.
.
KA SAN ME ZAI FITA BAKINKA
Abinda babu kokwanto a cikinsa shi ne duk wani mutum a gidansa sarki ne, kowaye kuwa, zan ba ka dan misali a kaina, a matsayina na malamin makaranta, na koyar da wani dan-sanda, to halin rayuwa sai na sami matsala na katin gidan talabijin wanda wani mutum ya zurma ni ciki, ina zaune aka ce ana gayyata ta a State CID, na tafi, sai na iske wannan mutumin da na sami matsala da shi, aka yi min wasu 'yan tambayoyi na fara qoqarin yin bayani, nan take wani ya daka min tsawa wai na dena daga masa murya, a lokacin na san ogansa dalibina ne, in ya zo wurina ka ga yadda yake maqe-maqen murya, to kowa a gidansa sarki ne.
.
Duk da cewa kowa ka gani a gidansa sarki ne zai yi kyau mu koyi yadda za mu yi magana da abokan hurdanmu, duk wanda yake da kayan sayarwa so yake ya qare, zai yi wahala hakan ta faru sai ya kusanto da abokan hurdarsa, wanda yake buqatar taruwar jama'a to ya ririta su yadda ba za su watse ba, na taba ganin wani mai sana'a da yake ce wa mai sayen "Kar Allah ya sa ka saya mana! In ka tafi dubunka za su saya kuma zai qare" ban san me ya hada su ba amma na tabbata wannan mutumin ba zai sake sayen kayansa ba, ba kuma zai bar wani nasa ya saya ba.
.
Iya magana da abokin ciniki ko abokan aiki fanni ne mai zaman kansa da ya dace duk mai hurda da jama'a ya koya, ana cewa "Shimfidar fuska ta fi shimfidar tabarma" wani ba magana mai dadi ba har murmushi zai yi maka, don dai ka sami natsuwa da shi, koda kuwa ka gaya masa maganar da bai ji dadinta ba, na ji an ce wa wani mai nama "Kamar da qura a kai!" Sai ya ce "A kansa aka yi yaqin Badar" fuskannan a murtuke ba alamar dariya, in zan kawo irin wadannan misalan suna da yawa, don wata mata da take waina mutane suna son abincinta amma da masifarta take korarsu.
.
Wani a makaranta yake aiki sai wani ya kawo dansa yake tambaya ko gwamnati ta amince da makarantar, da bude bakinsa sai ya ce "Ranka ya dade in ba za ka iya ba ka tafi wani wurin mana, wannan wace irin tambaya ce haka, gwamnati ba ta yarda da mu ba kawai haka sai mu zo mu bude makaranta?" Haka mutumin ya ce "Allah ya ba ka haquri" ya ja yaronsa ya tafi, sai mutumin ya ci gaba da cewa "Irin wadannan asali ba yaran suka kawo ba, neman magana da tunzura mutane suke yi" bayan shi ya kore shi.
.
Tabbas wasu rashin iya magana ne da mutane, wasu kuma rashin gwanancewa ne wurin hurda da jama'a, wasu tsabar wauta ce da rashin sanin qimar mutane, akwai kuma masu qarancin hangen nesa, sai dai ko ya mutum yake, iya magana wajinbi ne matuqar za ka yi hurda da jama'a, in ba haka ba sai a guje ka a bar ka kai kadai, in sana'a ce ka ga tana baya-baya ka rasa gane dalili, ai kai ne babban dalilin, in ma sarauta ce ka kasa iya bakinka sai yawan maganganu a kan abinda ya shafe ka da wanda bai shafe ka ba dole ka sami matsala, Annabi SAW ya riga ya ba mu mafita; mutum ya fadi alkhairi ko ya yi shuru.
.
Shi ya sa ake cewa ba mu iya sana'a ba, ai ba shiga inda ya dace ne ba mu iya ba, ba kuma rashin iya tsara lamura ne ba, har da ci da zuci da kuma rashin iya magana, za ka sami mutum a wurin sana'a amma fuskannan a murtuke ba ko alamar murmushi, wani kuma ya riga ya kafa wa kansa dokar ba zai yi magana sau biyu ba, in ya yi ta farkonnan sai ka yi da gaske kafin ka ji ya qara tanka maka, har ka ga wasu masu bidar kayan sun kama gabansu, kuma za ka ga ko a jikinsa, a ganinsa in ka tafi wani ma zai zo don haka tafiyarka ba matsala ba ce.
.
Akwai mutanen da in ka zo wajen sana'arsu sai ka ce kai ne sarkin, lallaba ka ake yi, komai ka ce kana so yanzu za a yi maka, in ma wurin sayar da kaya ne kana gama cinikinka za ka ji suna yi maka godiya, in ka ce kayansu da tsada cikin murmushi za su yi maka bayani har ka gane, ka ga an rabu cikin raha da dariya, irin wadannan don ka koma ko ka kira wani ba matsala ba ne, saboda shimfidar fuska ta fi shimdidar tamarma, sabanin wanda zai gasa maka magana kuma ko a jikinsa, mu koyi magana mai dadi kodon gyara lamuranmu.
Rubutawa:-Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```