*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 008```
.
Muna maganar sanin irin maganar da za ka yi da abokan cinikayyanka ne ko abokan sana'a ko na aiki, wannan kuma kamar yadda ya gabata a baya fanni ne mai matuqar mahimmanci yadda ba za a iya saka shi a daraja ta biyu ba, ko a littafammu na shari'a an nuna cewa iya magana don gamsar da mutum ma sihiri ne, don za ka iya tafiya da imaninsa ka sa shi ya amshi abinda bai yi niyya ba, ko ya biya abinda ba shi da shirin yin hakan, wani sa'i sai dai ka ji ana cewa an kwabsa wa mutum, wato an cuce shi ba tare da ya sani ba, qarqashin iya maganannan akwai wasu abubuwa kamar haka:-
.
1) Yarda da kai: Ka gamsar da mai sauraronka yadda zai tabbatar wa zuciyarsa cewa lallai abinda kake fadinnan haka yake ta wurin yi masa bayani cikin lafuzza masu dadi, qarya a wannan matsayin ba za ta taimaka ba, wanda ya fi kowa bin wannan hanyar ta gamsarwa don tallata kayansa shi ne magori, wato mai sayar da magani, koda kuwa maganin bera ne, in mai sayar da magani ya yi talla sai ka rantse da Allah in ka yi amfani da shi za ka warke nan take saboda tsabar iya magana, bokaye ma da dadin baki suke cutar mata da masu raunin zuciya, mutum ya ce zai yi maka kudi, bayan kai ma fa kudin za ka ba shi kafin ya yi, tunda shi ke yi wa mutane ya yi wa kansa mana, don me zai karbe dan na hannunka bayan taimakon jama'a yake yi? Amma in gilla maka qarya dole ka yarda saboda tsabar iya magana.
.
Irin wannan tunanin ba zai taba zuwa qwaqwalwar mutum a lokacin ba, haka zai dibi kudin ya miqa wa wani qaton banza ba tare da ya yi tunani ba, an riga an gamsar da shi kuma ya yarda, da yawan masu sana'a hanyar da suke bi kenan wajen gamsar da abokan cinikinsu, haka wasu jagororin addini, Allah ya kyauta, a ganina babban kuskure ne yin bayani don cutar da wani, in ka tsula wa wani kudi zai nuna wa wani ko ya gaya masa kudin da ya saya, daga ranar zai dauke ka macuci, ba zai sake dawowa ba, ba kuma zai kame bakinsa ba, ya dunga baza wa mutane kenan irin cutar da ka yi masa qila daga lokacin duk su qaurace maka saboda abinda aka fadi a kanka, gaya wa mutane gaskiya don tsare gaba, dadin baki don cutar da su kuskure ne.
.
2) Masaniya: Dole mai magana kan sana'a ko kayan kasuwanci ya kasance yana da masaniya sosai a kan abinda yake tallatawa, komai iya bayaninsa kuwa, in maras lafiya ya zo wurinka neman magani a qarshe ya fahimci ba ka san abin sosai ba ka bar qara ganinsa, ko kaya zai saya a wurinka in ya fahimci abinda kake gaya masa ba haka ba ne da qyar zai saya, kenan dole ne ka kiyaye abinda kake magana a kai, wasu daga bakinka suke qiyasta kyawun abu ko muninsa, an taba sanya wani ya yi wa wasu bayanin wata makaranta, gaskiya ya dan manta sunan makarantar, nan take masu saurarosa suka ce a canja shi in ba so ake su yi tafiyarsu ba, don ko sunan makarantar ma bai sani ba wani bayani zai yi musu gamsasshe su fahimce shi?
.
3) Rarrabewa: Dole ne mai bayani ya iya rarrabe lafuzzan da suke da kyau da munana, koda kuwa bambancin karin harshe ne, don wasu za su dauke ka mai batsa a maimakon su tsaya su saurare ka sosai su ji abinda kake so ka fada, in ka dauki kifi kana son ka yi bayanin jelarsa, a kano akan ce wutsiya, in ka ce bindi za su ji wani iri, kamar yadda mutanen Kaduna suke ganin wutsiya batsa ne bindi ya fi dacewa, kai mai bayani ka zabi kalmomin da masu sauraronka suke so su ji.
.
4) Haquri: Kai mai sana'a ko dan kasuwa ba dole ne kullum ka riqa jin abinda kake so ba, lokacin da mutum yake gaya maka munanan magana a wurin sana'arka, ko lafuzzan da ba ka son ji, ka haqura ka saurare shi har ya gama, kar ka yarda yana fadi kana maimaitawa, shi tafiyarsa zai yi in kun gama, kai kuma wurin naka ne, kayan ma naka ne, bai da asarar komai, in za ka iya ka yi murmushi, in ranka ya baci ka yi masa sai anjima, wannan ma zai tura masa haushi sama da a ce ka mayar masa da magana, don gardama ya ke so in ta so ku yi zage-zage, kar ka ba shi damar da zai ci nasara a kanka, yi amfani da qarfin zuciyarka.
.
5) Girmama fahimtar wasu: Masu sana'a a kullum sukan yi qoqarin nuna wa abokan hurdansu cewa sana'arsu tasu ce kuma sun fi kowa sanin kanta, in ka so ka nuna musu irin yadda kake so sai su yi maza su amshe maganar kafin ka qarisa, a dole sana'arsu ce ba za ka koya musu ba sun fi ka sanin kanta, abin haushi ma ba dole ne su yi maka bayanin da kai kake qoqarin yi ba, abinda ya dace ka saurari mutum har sai ya kammala abinda yake so ya fada sannan kai mai sana'a ka qara masa da abinda bai sani ba, ko ka gaya masa yadda abin yake, gardama da abokin sana'a ba taka ba ce kana da abubuwan yi da dama, kar ka bari ku sami sabanin fahimta.
.
6) Karbar gyara: Wani sa'i mai sana'a ko dan kasuwa ba ya son ka gaya masa aibin kayansa, yana ganin kana son ka kashe masa kasuwa ne, to bare dan kasuwan ma, a lokacin da ka dage sai ya fahimci kuskurensa yana iya yin fada da kai, maganar gaskiya hakan kuskure ne, kowa yana iyayin kuskure, in ka ji wanda yake son gaya maka aibin kayanka, ko aikinka saurare shi ka yi qoqarin gyarawa, ya fi a ce ya yi maka shiru ya je yana yayatawa jama'a kuma su zo su sami abin kamar yadda ya fadi, in mutum ya ankarar da kai ka saurare shi ka yi masa godiya, kuma ka yi haquri ka bi diddigin maganar da ya yi ka gyara, ba kamai da masa da baqa ba.
Rubutawa:-Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```