HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 06

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*

 ```// 006```
.
KYAKKYAWAN TANADI
Wani abu da ya zama dole a rayuwar mutum shi ne samun yanayi mai kyau ga abinda mutum yake buqatar ya yi, da kuma shigar da ta dace, suna daya daga cikin abubuwan da suka wajaba ga mutum, duk abinda zai yi ya dubi dacewa da kuma yanayi, ko sana'a za ka fara ka duba inda za ka yi din in mutanen wurin suna da buqatar kayan da za ka sayar, ba yadda za a yi wanda yake son gina makaranta ko dakin watsa labarai ya je tsakiyar kasuwa inda ake hayaniya ga qara gami da hargowa ya ce anan zai yi.
.
Wanda zai bude maqerar da zai riqa qera kayan gona to zai fi kyau ya zauna inda manoma za su riqa ganin abinda yake yi, don wani wucewa kawai zai yi in ya ga abinda yake so zai tsaya ya saya, ko in zai dawo ya riqo kudi, zan ba da misali daya, wani bawan Allah ya wallafa wani littafi da yake koyarwa game da mutuwa, tun daga rashin lafiya, da yadda ake jinya zuwa fitar rai, wankan gawa, ginin qabari da zaman makoki, littafi ne mai matuqar mahimmanci.
.
Zai yi kyau musulmi ya mallake shi ya yi nazari don sanin yadda zai suturta waninsa, sai dai ya yi wa littafin suna "MUTUWA" ga gawanan cikin likkafani an dora ta a kan anna'ashi, na ce wa mai sayarwan da za ku canja sunan littafin da hoton da aka saka a bangonsa da littafin ya fi shiga, misali a sanya fure a maimakon gawa, sunan kuma a ce "Tafiyar da ba makawa" ya ce ai komai ya yi daidai, ko ba a gaya wa mutum ba ya san cewa maganar mutuwa ake yi da abinda ya shafe ta.
.
A taqaice dai wallahi littafinnan qwara daya sai da ya gama cin dukar rana ya qoqe ba wanda ya saya, kuskuren wajen nuna wa mutane abinda ba sa son gani ne, duk wanda ya kalli bangon littafin zai yi wahala ya yi sha'awar siyansa, akwai wata yarinya da take tallar abinci, wallahi abincinta akwai dadi ga arha, komai kake so akwai, amma yanayin kayan da take sakawa, da wurin da take zama, da nau'in abincin da mutanen wurin suke buqata ya sa sam-sam ba a sayen abincinta, ga masu abincinnan a wurin ko kusan nata bai kai ba amma suna samun ciniki ba kadan ba.
.
Sun gyara shagon, ga kujeru da teburi, fanka na kadawa, a gefe ga firinji, na ci abincin wata a cikinsu sau daya ban qara ba, wancan ta farkon da za ta riqa kawo abinda ake buqata a hankali ta kwaikwayi wadannan, ta kiyaye dadin abincinta kar ta canja, tabbas sai ta qwace komai, akwai kuma lokacin da aka zo daukar malamai aiki, ana neman malamin Turanci, an sami wani Bayerbe komai ake so yana da shi har da qari, amma yana da qasumba, ga shi ya zo da jallabiya da wando rabin qwabri da takalmi silifas.
.
Wannan shigar kawai suka kalla suka manta da duk sifofin da yake da su, wai da na tambaye su dalili sai suka ce ba addini zai riqa koyarwa ba, wannan ya sa ban yi mamaki ba da na ga takardar wata da take neman aiki a wani gidan talabijin ta rubuta cewa ita fara ce kyakkyawa, na tabbata da gidan Radiyo ne qila sai ta ce tana da daddadar murya, wannan ma abin nema ne a wurinsu can, duk abinda za ka yi ka dubi buqatun jama'a da kuma yadda za su kalle ka.
.
An yi wani zamani a qauyemmu lokacin da fulani suka rabu biyu, akwai masu sayar da nono a kwano da masu sayarwa a qwarya, masu sayarwar a kwano sukan ci ado ka gan su tsab-tsab koda yaushe amma fa suna da tsada, na qwaryar ne dai da arha, na tabbata shigar masu sayarwan a kwanon da yarda da kai da yadda suka qawata sana'ar suke ganin abinda ya dace a yi kenan, domin duk da tsadarsu da komai wasu sun fi natsuwa da su, ba su sayen nono sai a wirinsu, ko lauyoyi da likitoci gami da manyan ma'aikata ba wani abu ya sa kake ganinsu tsab-tsab ba sai inganta ayyukansu, ana qimanta mutum wani sa'in da irin shigar da ya yi ne.
.
Ka lura da kyau ka gani, ko tsayuwa ka yi wurin wanda ya fito tsab za ka ga shi ake girmamawa, na taba yin tafiya wani lokaci da maigidanmu, akwai kuma ma'aikatammu, cikinsu akwai wani Bakatsine da ya sha shakwara da jamfa, duk inda muka shiga sai ka ga an tsallake mu an fuskance shi, ba wani abu ya fi mu ba illa irin shigar da ya yi, ana ganin shi ne ogan gaba daya, zaben wurin aiki, shigar ma'aikacin, nau'in irin aikin duk abin dubawa ne, mu tara a gaba kan wannan batun. 


Rubutawa:-Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)