*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 10```
.
BA WA QWAQWALWA DAMAR AIKI
Mutane sun karkasu zuwa gidaje daban-daban, akwai masu qoqari wadanda kullum cikin tunanin bunqasa ayyukansu suke yi, in dan kasuwa ne wanda yake sayar da gwanjo, yakan fara tunanin cewa nan gaba fa zai iya tsallake wannan sana'ar zuwa wace ta fi ta, kamar sayar da sabbin kaya wadanda aka yiwo odarsu daga qasashen waje, in mai sayar da takalma ne a bakin titi yana bin motoci da gudu, zai fara tunanin cewa nan gaba fa jarinsa zai yi yawa zai kama shago, zai zama babban dan kasuwa har a mutane zu riqa zuwa suna sarin kaya a wurinsa.
.
In kuma malamin makaranta ne zai fara tunanin zai zama babba har ya yi fice a fagen ilimi, zai gina makaranta tasa mai cin gashin kanta, in karen mota ne yana tunanin zai zama direba zai sami mota tasa ta kansa, zai zo ya sayi motoci nan gaba ya dauki direbobi yana biyansu, wadannan abubuwa ba su rabuwa da zuciyoyin gwarazan mutane, wadanda duk abinda za su yi suna tunanin gaba, kamar mutum mai qaunar ibada kullum a masallaci, har ya fara burin a ce shi ne ladanin masallacin, yau da gobe ya zama na'ibin limamin, ko a ba shi limanci a wani masallacin, da yawa in mutum zai kama haya saboda zai yi aure za ka ga ya fara tunanin inda yaransa za su riqa kwana da tarbiyar da za su samu a matattarar, bayan ko auren ba a daura ba, tsari kenan.
.
Da yawa mutane masu himma sun sami abinda suke buri, wani zai gaya maka shi babban soja ne, kuma wallahi tun yana qarami bai da buri sai aikin sojan, wani zai ce maka likita ne shi, tun yana qarami burinsa kenan, wasu lamuran Allah kan dubi zuciyoyimmu ne ya biya mana buqatummu, dubi dai waqa da ake ganin abar banza ce, na dubi Hauwa Kululu wace Mamman Shata ya yi wa waqa, tana cewa tun tana yarinya ba ta aikuwa sai in mutum zai yi mata waqar Shata, asali ita yariya ce qarama, ba ita ce mai sayar da tuwon ba babarta ce.
.
Lamarinta ya riqa ba masu sayen tuwon babarta al'ajabi, kwatsam sai ga Mamman Shata din wata rana ya sauka wurin babarta, aka ba shi labari kuma aka nemi ya yi mata waqa, Shata ya zauna ya waqe ta fes, burinta ya cika, amma fa ba arha ta sami wannan daukakar ba, sai da ta tsaya kan burinta har ta kai ga gaci, sauran lamura da kake gani a rayuwa duk haka suke, ba yadda za a yi mutum ya kai ga biyan buqata ba tare da ya tsaya qyam kan abinda yake so ba, kullum tunaninsa shi ne ya zan kai ga wannan qudurin nawa?
.
Burina a ce na zama malami, na fara koyarwa ne a makarantar Islamiyya ta dare, a hankali har na dawo ta safe, na koma furamare, na fara karantarwa a sakandare da ta manyan mutane, na karantar a kwaleji kafin yanzu na komo jami'a, tafiyar ba mai sauqi ce ba kamar yadda na karanto haka, akwai jarabowoyi a tsakiya kala daban-daban, wasu har ba ka son ka tuna su, ba ka qaunar ka ga wanda ya san su, burin mutum a zuciya kawai ya isa wurin da yake hari, kuma zai isa din amma sai da taimakon Allah SW, kenan tun farko shi ne mutum zai fara kamawa, in ya amince maka dole a baka, duk abinda za ka yi kar ka manta da mahaliccinka.
.
A cikin mutane akwai wadanda suke son ci-gaban, kuma suna ganinsa tare da wani, amma ba sa qaunar su motsa, ba sa iya yin tunanin cewa za su zama wani abu nan gaba, wanda yake yankar farce dole ya saka cewa zai zama wani abu yadda nan gaba shi ma za a zo a yanke masa, bunqasa sana'a dole ne in ba haka ba nan gaba za a rasa mai yi, amma ci-gaba ma wajibi ne, ba yadda za a yi ka ce kaza na gada kansa zan mutu, bai zama dole sai ka canja sana'a ba, amma ka yi tunanin ya za ka bunqasa shi har mutane birjik su qaru da kai?
.
Ba yadda za ka bunqasa gadon mahaifinka sai ka yi tunanin kawo na'urorin da za su sauqaqa aiki su inganta shi ta yadda za a riqa yi da yawa, ko a canja salo, duk abinda ka sani a duniyannan za a iya inganta shi, na san wani yaro da ya taso a gaban mahaifinsa tela, yanzu ya zama babban tela ya kawo manyan kekuna masu yi wa kaya ado, da haka ya mallaki gida na kansa da ma'aikata masu yawa, sana'ar dinkin ce dai ba a canja ba, amma an qawata ta, an habbaka ta, an inganta ta, wannan ya sa aka qara samun dafifin jama'a dake burin ganin an yi musu dinki a shagon.
.
Duk wani babban mutum da kake gani wanda ya ci nasara a rayuwarsa ta hada-hada, ko cinikayya, ko wani fanni na aiki ko sana'a in zai gaya maka hanyoyin da ya bi don ganin ya cimma burinsa za ka taras sai da ya ci baqar wahala, anan akwai abubuwa guda biyu:-
1) Ya sa abin a ransa don ganin ya cimma burinsa, ya yi ta bin hanyoyi daban-daban don ganin hakan ya wakana, ko dai karatu, ko mutanen da yake ganin za su taimake shi, ko bibiyar shawarwarin da za su isar da shi.
2) Aiki tuquru kan jiki kan qarfi, yin amfani da kudi wajen sayen kayan aikin da in ba a samo su ba aikin ba zai yuwu ba.