TAMBAYA
=========
Assalamu Alaikum.. Allah ya taimaki malam tambaya ce dani kamar haka.. Acikin jerin sunayen matan sayyidina umar r. a akwai Mai suna Ummu khulsum bint Abubakary. To tambayar anan itace : Shin wane Abubakar din ne? Sayyidina Abubakar ko kuma wani Abubakar ne daban?
Tambaya ta biyu itace.. Akwai wani hadisi da manzon Allah s a w ya bamu labarin wani mutum da yace wa 'ya'yan sa idan ya mutu su qona shi sannan su dauki tokar rabi su zuba a cikin teku rabi kuma su sheqe don kada ya hadu da ubangiji saboda yace idan har ya hadu da ubangiji to zai yi masa azaba.. Har daga qarshe manzon Allah s a w yace Allah zai tayar dashi ya tambaye shi dalilin haka, har Allah s w t yace to ya gafarta masa.. Kuma hadisin ya nuna bai ta'ba aikin alkhairi ba.. To tambaya ta anan itace shin aikin alkhairin da aka ce bai ta'ba yi ba shin har da Sallah ko kuwa?
AMSA
=====
Ban san umar ya taba auren yar gidan sayyadina Abubakar ba, haka nayi ta bincike cikin littattafan tarihi ko zan sami wannan bayanin, amma ban samu ba gaskiya.
Abinda nake dashi, anan shine, idan ka duba littafin ANNASABU WAL MASAHARATI BAINA AHLUL BAITI WASSAHABA " shafi na 328. Matan da sayyadina umar ya aura sune,
1. ZAINAB BINTU MAZ'UM, yar uwar usman ibn maz'um.
2. UMMU KULSUM BINTU JARUL ALKUZA'IYYA.
3. UMMU HAKEEM BINTUL HARIS ALMAKZUUMA.
4. JAMEELA BINTU SABIT wadda yar Uwa ce ga AASIM IBN SABIT.
5. ATIQAH BINTU ZAID.
6. UMMU KULSUM BINTU ALIYU BIN ABI DALIB.
Wadannan suna matan sayyadina umar Dan khaddab.
Sabida haka, kenan sayyadina Umar sirukine ga SAYYADINA ALIYU IBN ABI DALIB, Gashi kuma yan Shi'a suna zagin sayyadina Umar siruki ga sayyadina Aliyu.
'Yayansa kuma sun hada da.
1. Ruqayya
2. Hafsat matar manzon Allah saw.
3. Fatima, wadda mata ce ga Abdurraahman ibn zaid.
4. Zainab, wadda itama mata ce ga Abdurraahman ibn mu'utamad.
5. Abdullahi, Wanda shine na biyu daga cikin wadanda sukafi kowa rawaito hadisin manzon Allah saw. Daga abi huraira sai shi.
Kissar wannan bawan Allah da ka kawo, tana cikin sahihul Bukhari, kitabu Ahaadisul Anbiya da Kuma kitabuttauheed, haka Muslim ma ya kawota cikin sahihun sa a kitabuttauheed, sannan Doktor mustapha Murad ya kawo wannan Kissar a cikin littafin KULUQUL MU'UMIN shafi na 95.
Kamar yadda ruwayar ta nuna, Wannan mutumin bai taba aikata duk wani nau'in Alkairi ba a rayuwarsa. Domin haka. Manzon Allah saw ya Nassanta, kuma manzon Allah saw cewa yayi, anyi wani mutum kafin zuwan wannan al'ummar, kaga kenan ba ma a wannan zamanin aka yishi ba.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876SECOND REMINDER. Thursday. FIX YOUR WORLD BY PLACING ALLAH, HIS MESSENGER AND THE QUR'AN IN THE RIGHT PLACE IN YOUR HEART. BismilLah
An Imam was struggling to prepare his Friday sermon and didn't want to be disturbed by his five year old daughter, so he removed a map of the world from his study, tore it into pieces and gave it to her to assemble with the promise that he would answer all her questions and play with her when she was done. He knew she would never be able to fix it.
To his amazement, in less than five minutes, she returned to him in his study with the map in perfect shape, every continent and every country in its place. The surprised father asked, ''Honey, you don't know anything about geography, so how did you fix the world so easily and quickly? The five year old girl smiled sweetly and replied, ''The picture of of THE HOLY QU'R' AN and the inscription LA ILLAHA ILLALLAHA MUHAMMADU ROSULULLAH was at back of the map and I knew that if ALLAH, His MESSENGER and QUR'AN are put in the right place, the whole world would be in perfect shape'.
That was just the right inspiration he needed for his sermon. He thanked his daughter and prepared a powerful sermon on the subject: "Fix Your World By Placing ALLAH, His MESSENGER and the QUR'AN in the Right Place in your heart ".
To whoever is reading this message, just place ALLAH, His MESSENGER and QUR'AN in the rightful place and your life will be in order.
I hope you understand this just like I do. Share and spread it to the world, let them know that THEIR WORLD CAN NOT BE COMPLETELY FIXED WITHOUT ALLAH, HIS MESSENGER AND THE QUR'AN.
MAY ALLAH BLESS US ALL AND KEEP GUIDING US ALL. AAMEEN.