ZUWAN MUSULUNCI ƘASAR HAUSA 1

HAUSA PROGRAM

*ZUWAN MUSULUNCI KASAR HAUSA*

KASHI NA 1

*2/August/2020*

DAGA ; Muhammad Muhd Abubakar

A game da kasar Hausa tarihi ya nuna mana baa shigo mana da musulunci ta hanyar karfi ba. A'a musulunci ya shigo mana ne ta hanyoyin fataucin kasuwanci da kuma matafiya na sa-kai don neman tarihin kasa da da'awa ta wa'azi da kuma hanyar kaurace_kaurace na kabilu da al'umma daga wuri zuwa wuri kamar yadda ya gabata.

'Yan kasuwa 

'Yan kasuwa su ne suka fara shigowa da musulunci kasar nan, amma ta hanyar daidaikun mutane ne. Wasu ma sune ganin tun a farko karni na hijirar manxon Allah (S.A.W) musulunci ya fara saduwa da kasar Hausa ta gefen katsina zuwa kano, inda matafiya na kasuwanci suke bi daga wasu kasashe na larabawa. Su ne kuma suka shigo mana da musulunci ta wannan hanyar zuwa arewacin Nigeria.

#ASOF


Inayiwa dukannin musulmin duniya barka da sallah

AREWA STUDENT ORIENTATION FORUM


Post a Comment (0)