FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA 2


FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA 2

Duk da cewa an samu cece-kuce a tsakanin masu harkar fassarar fina-finan Indiya zuwa harshen Hausa da kuma wasu daga cikin 'yan masana'antar Kannywood, daga baya an zo an samu fahimtar juna inda komai ya lafa. Amma babban abin dubawa shi ne, wannan taƙaddama ta jawo hankalin masana'antar Kannywood zuwa tun tuni masu kallo ke so su kalla amma basu kalla ba. Wato sun fara kallon ƙalubalen da ke gabansu kuma sun fara ƙoƙarin gyarawa.

To mecece fassara?

Fassara ita ce canja wani bayani, suna ko abu daga wani harshe zuwa wani harshe ba tare da an canja ma'anar abun ba. Ita kuwa fassara tana da wasu ƙa'idojin da dole ne mai yinta sai ya kiyaye su. Na farko dai wajibi ne ya kasance mai fassara yana jin yaren da zai ɗauko bayanin daga gare shi da kuma yaren da zai yi fassarar. Na biyu kuma dole ne ya kasance ya san al'adun mutanen da ke amfani da Harshen sosai. Sannan abu na uku kuma shi ne; ba a yin fassara ta kalma da kalma, ana duba ma'ana ne.

Haka kuma fassara ta kasu kashi biyu ne, akwai mai 'yanci da kuma maras 'yanci. Fassara mai 'yanci ita ce irin fassarar da ake yi wa fina-finan Indiya a nan Nijeriya zuwa harshen Hausa da sauransu. Dalilin ba ta wannan suna kuwa shi ne; mai fassara yana da 'yancin canja wasu kalmomi zuwa wasu matuƙar dai ma'anar za ta fito. Misali; kamar yadda ake amfani da kalmar "shiƙa" a madadin kalmar "kisa" da sauransu. Ita kuwa fassara maras 'yanci ita ce fassara irin wacce mai fassarar ba shi da ikon canja komai yayin fassarar. Misalan irin wannan fassara su ne kamar fassarar abubuwan da suka shafi magani, shari'a, Addini da dai sauransu. Dalilin da ya sa aka hana mai fassara 'yancin canja wani abu kuwa shi ne, kuskure kaɗan idan aka samu wajen yin wannan fassara tana iya jawo mummunan sakamako.

To kenan abinda masu fassarar fina-finan Indiya zuwa harshen ke yi na sauya wasu kalmomin zuwa wasu ba laifi tun da dai bai canja ma'anar ainahin saƙon da fim ɗin ke isarwa ba. A maimakon hakan, sai ma dama da ya bayar domin samun sabbin kalmomin da za a haɓaka rumbu ko gandun kalmomi da su. To suma masu fassarar sun kasu zuwa gida biyu. Akwai masu yin nagartacciyar fassara akwai kuma masu yin kan kura. Masu yin nagartacciyar fassara su ne waɗanda suke ba fassarar dukkanin haƙƙoƙinta waɗanda na ambata da kuma waɗanda ban ambata ba. Su kuwa masu yin kan kura, su ne masu yin akasin hakan. 

Dangane da muryoyi kuma da ake sakawa iri daban-daban, shima duk yana daga cikin haƙƙoƙin fassara ne da ake ƙoƙarin saukewa. Domin babu yadda za ayi a ce muryar mutum biyu ko sama da haka ta zama iri ɗaya sak a cikin fim. A taƙaice dai, suna saka muryoyin ne dai-dai da ɗabi'ar mutanen da ke jagorantar shirin. Misali: Muryar matashi mai cike da izza wa jarumi, murya kakkausa mai cike da jiji da kai wa azzal, murya sassanya mai jan hankali wa budurwar jarumi da dai sauransu. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Post a Comment (0)