MUHIMMIN SAKO ZUWA GA YAN SHEKARA ARBA'IN
Assalamu alaikum warahmatullah,Ina fatan kun tashi lafiya , Allah ya kara lafiya da suttura duniya da lahira.
Bayan haka,hakika rayuwa cikin musulumci da koshin lafiya niimomi ne masu girma da babu abinda mutum zai yi sai dai ya yi ta godiya ga Allah Taala akansu tare da nuna gazawa da kaskaantar da kai a gare shi.
Shekaru arba'in a duniya wani zango ne mai matukar muhimmanci a rayuwa wanda Allah Taala ya nuna darajarsa domin a wannan lokaci ne yake aiko manzanninsa masu girma.Kuma a wannan zango ne mutum yake zama kamili a kusan kowane bangare na rayuwar sa,yake fara fahimtar hakikanin rayuwa a bisa yadda take musamman idan ya sami kyakkyawar kulawa da ingantacciyar tarbiyya a baya.
Lokaci ne da tunani yakan canja ,abubuwa da yawa na salon rayuwa da jiki su sauya.
A lokacin farin gashi (furfura) yake kankama a kai da gemu,wasu ma tun kafin wannan lokacin ake ganinta.
Wani daga wannan lokaci alamun tsufa suke fara bayyana a gare shi, amma kuma a ilimance ba za a ce da dan shekara arba'in tsoho ba , amma yanayin rayuwa da tunani da cimaka na mutum shi yakan sa ka ga yaro ya tafke, babba kuma ka gan shi kullum kamar yaro.
Waɗansu sukan firgice daga sun shiga shekara ta arba'in su dauka su tasu ta kare ,mutuwa kawai suke jira musamman idan furfura ta yi gaggawar fesowa, wannan kuskure ne domin In shekara 60 ko 70 aka yanka masa zai yi a duniya ai ka ga yana da sauran shekaru 20 ko 30 wadanda zai iya yin abubuwa masu kyau da yawa a cikinsu.
Tsige furfura ko aske gemu don kada a ga furfurar mutum a ce ya tsufa haramun ne,ai hakikanin tsoho shine wanda zuciyarsa da tunaninsa suka tsufa suka daskare,kuma ita furfura ado ce ga mumini kuma alama ce ta nutsuwa wacce take haifarwa da mutum kwarjini a idon mutane musamman In an tsare mutunci.
Babu laifi a rina furfura da jar kala ko ruwan ɗorawa,amma a guji rina ta da baki.
CANJA SALON RAYUWA
Ya kamata ga dan shekara arba'in zuwa sama da ma wanda ya kusa kaiwa arba'in ya canja salon rayuwarsa kamar haka:
1.ZUZZURFAR TUNANI
Mutum ya zaunar da kansa ya yi dogon tunani akan rayuwarsa ya gayawa kansa gaskiya ya tambayi kansa tambayoyi uku:
_ 1_Shin me na aikata a shekaru arba'in da suka wuce ?Wadanne nasarori na samu kuma wadanne matsaloli na fuskanta a rayuwa ta.?
_2_Shin yanzu a wane mataki nake na rayuwa ,me nake yi ?
_3_Shin nan gaba me nake son yi,yaya kuma zan yi shi ?
2.TUNANIN ABINDA ZA KA BARI
A yayin amsa tambaya ta Uku ka yi tunani da aiki na gaske kan me za ka bari bayan mutuwarka wanda za.a.rinka tuna ka da shi ana yi maka addu'a saboda amfanarsa da mutane suke yi ?
Wannan abu ne mai yiwuwa saboda mu dubi dimbin alhairi da shugaban halitta ya bar mana mara yankewa wanda ya fara shi ne yana dan shekara arba'in,ashe In za mu yi koyi da shi ba za mu ce mun makara ba.
3.TUNANIN WA ZA KA BARI
Lallai a duk matakin da kake kai na rayuwa ka fara tattali da horon wadanda za ka tafi ka bari domin ɗorawa daga inda ka tsaya a ayyukan alhairi.
In kai Malami ne malamai nawa za ka mutu ka bari a cikin dalibanka wadanda za su ci gaba da gwagwarmaya bayan mutuwar ka?
In kai dan kasuwa ne ko wani mai sana'a ko maaikaci ,attajirai nawa ko kwararru za ka tafi ka bari wadanda da an gansu za a tuna ka a yi maka addu'a?
Kai har yayanka ka yi tunani kuma ka tsara ka kuma yi aiki don ganin wane irin samari da.yan mata da iyaye za ka tafi ka bar wa alumarka ?Wace gudummawa za su bayar wajen ci gaban zuriarka da al'umma gaba daya ?
4.CANJA GABA DAYAN SALON RAYUWA
Kusan kowane bangare na salon rayuwar dan shekara arba'in zuwa sama da wanda ya kusa kaiwa arba'in yana da bukatar sake nazari da canjin salon gudanar da shi.
Wadanne bangarori sun hada da :
1.CAJA BATIRIN IMANI
Ya kamata a kara yawaita ibadu masu kara imani da tausasa zuciya,In kuma ba a yi to a fara.
Misali Kiyamullaili,farkawa cikin dare domin yin salla da addu'a,a ƙalla awa daya ko rabin awa kafin sallar asuba domin a ribaci wannan lokaci mai matukar faida da albarka.
Yin azumin nafila ko da sau uku ne a kowane wata.
Yawaita aikin hajji da Umara ga wanda yake a kusa da garin Makka ban da na nesa.
Jaddada tuba da yawaita istigfari .
2.IN AN GIRMA.A SAN AN GIRMA
Ya kamata wanda ya kai wannan mataki na rayuwa ya san fa yanzu ya zama babba watakila an fara tara ya'ya,kuma manya sun fara tafiya nauyi ya fara yin yawa,to ya kamata a bar hululu a yi sallama da halaye marasa kyau musamman shaye shaye, da tabe tabe,da dauke dauke da fitintinu da yan uwa da makota da abokai ,a yi sulhu da kowa a rungumi zumunci ,a tallafawa Yan uwa da sauran mabukata.
3.ME KA YI WA ADDININKA ?
Ya kamata kowa ya yi wa kansa tambaya wace irin gudunmawa yake bayarwa ga addininsa ?Kuma me zai tafi ya bari na ci gaban addini bayan rasuwarsa ?
Wani sai ya zo duniya ya koma bai yi wa addininsa wani abin a zo a gani ba,sai dai kawai ya tara kudi ya sayi kasa ya yi abubuwa kala kala ya tafi shine nan.Lallai ya kamata a sake tunani, musamman wadanda Allah Taala ya ba su dama ta dukiya ko ilimi ko mukami.
Za ka iya shiga kwamitin wa'azi da musuluntar da wadanda ba musulmi ba da sauransu.
4.GEMU BA YA HANA KARATU
A yanzu bayan ka girma za ka iya riskar abinda ba ka samu damar riska ba a baya na karatun addini da na zamani.
Za ka iya shiga halkar koyon karatun Alkur'ani da haddace shi,da kuma majalisai ko makarantun ilmi.
Akwai manyan Malamai da sai da suka girma suka fara neman ilimi kuma suka zama bijimai hamshakan malamai irinsu Ibn Hazmi,da Izzuddin Ibn Abdussalam da Al Imamai Alqaffal.
Haka kuma za ka iya komawa.makaranta domin kammala karatun boko da yanayi y dakatar da shi ko da kuwa ta salon karatu daga nesa ne ko kuma budaddun jami'o'i.
Ka sani cewa ƙwaƙwalwar ka tana da bukatar abinci lafiyayye wanda shine ilimi.
Yi kokari akalla a kullum ka ware awa guda domin karatu ,ba lallai sai littatafan larabci ba,akwai littafai na Hausa masu yawa da dimbin faida
5.KARA INGANTA ZAMAN IYALI
Anan ma ya kamata a kara nazari akan yanayin zaman da ake yi,a kara karfafa hanyoyin zaman lafiya a toshe duk wata kafa ta fitina da tashin hankali.
A kara kulawa sosai da tarbiyyar yaya musamman manyan cikinsu,a rinka ba su lokaci ana zama da su ana tattaunawa da su.
Idan da bukatar kara aure a yi shi cikin fahimta a yi adalci kuma a tabbatar za a iya yi banda dage banda rigima.
Sha'awar jinsi ita ce karshen abinda yake karewa ga mutum,wani ma sai ya tsufa sai sha'awar ta dawo kamar ta matashi (balagar tsufa) ya kamata ma'aurata da iyalansu su fahimci haka kada a zalunci kowa.
6.KULA DA LAFIYA
Ginshikan samun lafiyar jiki da karkonsa sune:
1.Cin lafiyayyen abinci __A yawaita cin ganyayyaki da kayan marmari na asali ba na gwangwani ko kwalaba ba.A rage cin jan nama. A guji shan taba sigari da giya da dukkan kayan maye.A tsara lokutan cin abinci.A rinka yawan shan tsaftataccen ruwa.
2. Samun wadataccen hutu__Akalla a kullum a samu barcin awa shida ba tare da yanke wa ba,a wurin da iska take gewayawa,In da hali a hada da barcin rana koda na mintinan 15 ne.
A gujewa tara barci aka musamman saboda kawai ana kallo ko amfani da waya.
3.Kaucewa yawan bacin rai__Mutum ya guji duk abinda zai jawo masa fushi da bacin rai.In kuma abin ya faru ya yi hakuri ya kai zuciya nesa.
A daina riko da hassada da gaba,wadannan halaye suna saurin tsofar da mutum da haifar da cututtuka musamman na damuwa da karya garkuwar jiki.Yawan murmushi da farin ciki yana inganta lafiya da samun tsawon rai a duniya.
4.Motsa jiki__ Lallai a kullum mutum ya tabbatar yana motsa jikinsa musamman ta hanyar tafiya a kasa ,akalla tsawon.minti 40 a kullum.
Wadannan sune muhimman sakonni da masana suke isarwa ga yan shekara arba'in zuwa sama da waɗanda suke dab da shiga arba'in ,domin tattalin nasarori da aka samu da kara habaka su ,da kaucewa matsalolin da aka gamu da su a shekaru masu zuwa,da kuma samun damar kyakkyawar cikawa da barin zuri'a managarciya.
Domin samun cikakken bayani duba
جدد حياتك رسالة إلى من جاوز الأربعين للدكتور محمد موسى الشريف da
صحتك بعد الاربعين المعصومة علامة da
جدد حياتك لمحمد الغزالي da
ريح النسرين فيمن بلغ الاربعين للشيخ محمد بلغوا بن عثمان بن فودي
Ina rokon Allah Taala ya i ganta rayuwar mu ya kyauta karshe mu ya albarkaci zuriarmu ya tsare imaninmu gaba daya.Maasallam.