SHARHIN FIM ƊIN BHAIRAVA


SHARHIN FIM ƊIN BHAIRAVA 


Bairavaa fim ɗin Indiya ne da aka fitar a shekara ta 2017 cikin harshen Tamil. Bayan an fara ɗaukar shirin a farkon shekara ta 2016, an ci gaba da aikin shirin a ƙarƙashin suna Vijay 60, inda daga baya aka canza masa suna zuwa Bairavaa a cikin watan Satumbar 2016. An saki fim ɗin a duniya baki ɗaya a ranar 12 ga watan Yuli 2017. Sai da aka yi kwanaki 50 cif ana kallon shirin a gidajen kallo bayan fitarsa kuma ya taɓuka abin a zo a gani ma a harkar kasuwancinsa. 

• Bada Umurni - Bharathan

• Ɗaukar Nauyi - B. Venkatarama Reddy

• Labari/Rubutawa - Bharathan

• Sauti - Santhosh Narayanan

• Horas Da 'Yan Wasa - M. Sukumar

• Tacewa - Praveen K. L.

• Kamfanin Da Ya Shirya - 
Vijaya Productions

• Kamfanin Da Ya yi Dillanci - 
Sri Green Productions

• Ranar Fita - 12 January 2017

• Tsayin Shirin - Mintuna 169

• Ƙasa - India

• Harshe - Tamil

• Kasuwancin Box office - ₹114 crore

Bairavaa wani jami'in karɓar haraji ne a bankin ICCI da ke garin Chennai. Mutum ne mai gaskiya wanda a shirye yake ya yi amfani da kowace hanya wajen amso kuɗaden da masu karɓar bashi suka amsa. 

Watarana ana bikin 'yar manajansa sai ya haɗu da Malarvizhi wacce ita kuma ɗalibar kiwon lafiya ce daga garin Kallidaikurichi da ke yankin Tirunelveli kuma nan take ya kamu da son ta. Yayin da ya je madakatar Koyambedu domin ya bayyana mata soyayyarsa kafin ta bar Chennai, sai ya ga wasu gungun 'yan daba sun kewaye ta da nufin za su kashe ta saboda suna zargin tana da sa hannu akan harin da aka kai wa ɗan gidan Minista Charan. Ana cikin haka, sai suka fasa kashe ta sakamakon kiran da suka samu daga PK cewa kada su taɓa ta. Hakan ya sa Bhairava ya tambayi Malar abin da ke faruwa in da ita kuma ta zayyane masa komai. 

Malar tana karatu ne a makarantar PK Medical College da ke Tirunelveli, to shugaban makarantar wato PK wani babban ɗan daba ne kuma ɗan siyasa a lokaci guda. Shi da na hannun damarsa Kottai Veeran suna aikin daba da siyasa tare. To ita wannan makaranta babu kayan aiki a cikinta, gininta ba mai nagarta bane kuma babu isassun ma'aikata da likitoci. Wannan ya sa Malar da ƙawarta Vaishali suka shigar da ƙorafi wa MCI, in da shi kuma ya sha alwashin saka makarantar a baƙin littafi bayan ya ga matsalar da idonsa. To amma PK saboda ya kare mutuncinsa sai ya haɗa baki da wasu jami'an MCI akan su soke takardar dakatarwa da aka zana, shi kuma zai basu damar yin lalata da ɗaya daga cikin 'yan matan makarantar. 

Bisa tsautsayi kuwa sai aka zaɓi Vaishali, in da washegari sai tsintar gawarta aka yi bayan an mata fyaɗe. Mahaifin Malar wani ɗan sanda ne mai gaskiya, hakan ya sa ya fara bincike akan alaƙar da ke tsakanin PK da mutuwar Vaishali, amma sai PK ya kashe shi shima. Bayan mutuwar mahaifinta sai Malar ta kai PK ƙara kotu in da alƙali ya yanke hukuncin cewa kada a kore ta daga makaranta kuma kada wani abu ya sameta har sai an kammala wannan shari'a. Ko da yake PK ya yarda da wannan hukuncin, sai ya dinga kai wa Malar farmaki ta hanyar malaman makarantar da kuma yanke lantarki da wutar da ke yankinta kuma ya sha alwashin da zarar an gama shari'ar ya samu nasara zai kashe ta. 

 To a wajen ɗaurin auren ne Malar ta miƙa bidiyon da ke ƙunshe da hujjojin mutuwar Vaishali ga Charan, akan cewa tun da shi ɗan gidan Minista ne zai iya taimakawa a binciki bidiyon. Amma sai PK ya aika yaransa suka ƙwace bidiyon kuma suka maƙala wa Malar laifin. Da Bairavaa ya ji wannan labari, sai ya yanke shawarar zai taimake ta don haka ya bi ta suka tafi Kallidaikurichi tare. 

Ta hanyar basaja a matsayin mai karɓar haraji Bairavaa ya shiga gidan PK ya yi bincike har ya samo hujjojin da yake buƙata. Ba a jima ba kuwa sai PK ya fahimci cewa Bairavaa fa so yake ya ga bayansa, hakan ya sa aka fara tata-burza a tsakaninsu in da daga ƙarshe dai PK ya samu nasarar karɓe hujjojin ya kuma lalata su. Ko da yake Bhairava ya rasa hujjojin, ya yi ƙoƙarin samun ƙarin kwanaki biyar kafin a kulle shari'ar 

To ana cikin haka ne kuma sai matar Kottai Veeran ta mutu, don haka sai Bairavaa ya yi amfani da son da Kottai Veeran ke yi wa matarsa domin gabatar da shi a matsayin shaida akan shari'ar da ake yi. Shi ne sai ya canja wa PK robar shaƙar iskarsa da sinadarin nitrous oxide. PK shi kuma ya shaƙa ba tare da ya sani ba kafin ya je bikin janazar matar Kottai Veeran. Hakan ya sa shi dariyar babu gaira babu dalili har aka gama janzar, hakan ta sa shi kuma Kottai ya fusata ya juya masa baya kuma ya karɓi yayin Bhairava na zan bada shaida a kotu. Saboda jin haushin abin da ya yi mai, sai PK ya tari Kottai Veeran inda suka gwabza har ya kashe shi. 

Daga nan sai Bairavaa ya yanke hukuncin kashe PK kawai kowa ya huta saboda ta haka ne kawai zai iya rama wa Malar da Vaishali abin da aka yi musu. Don haka sai ya ƙala wa PK sharrin cewa yana shirin kashe Firimiyan India yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kudankulam domin dasa aikin wani makami mai linzami. Ai kuwa nan take labari ya watsu a gari har ta kai an bada izinin da an ga PK kawai a harbe shi. Da dai PK ya ga an rutsa shi, sai ya yi nufin ya kashe Bhairava amma sai bai yi nasara ba. Daga nan kuma sai Bhairava ya yi shiga irin ta kwamandawan NSG ya sace da na gaskiyar waɗanda suka zo kashe PK. 

A ƙarshe dai an bayyana cewa Malar ce ke da gaskiya, an kama yaran PK an kulle sannan aka kwashe ɗaliban PK Medical College akai kai su wata kwalejin. 

Ko da yake Bairavaa yana goyon bayan gina makarantun kuɗi, ya ce abu ne mai muhimmanci a shugaban wannan wuri ya zama mai gaskiya kuma nagartacce domin ya tabbatar da tsaron lafiyar ɗalibai da kuma samun ingantaccen ilimi. 

Jaruman Shirin 

• Vijay - Bairavaa

• Keerthy Suresh - Malarvizhi

• Jagapathi Babu - Periyakannu/ PK

• Daniel Balaji - Kottai Veeran

• Sathish - Shanmugam

• Thambi Ramaiah - Narayanan

• Mime Gopi - Karuvadu Kumar

• Sija Rose - Poongodi

• Harish Uthaman - Prabha

• Aparna Vinod - Vaishali

• Papri Ghosh - Shailaja Venkatesan

• Sriman 

• Aadukalam Naren 

• Sharath Lohitashwa - Union Minister

• Roshan Basheer - Charan

• Rajendran - M. Rajendran

• Y. G. Mahendran - R. Venkatesan

• Vijayaraghavan 

• Seema G. Nair 

• G. Marimuthu - Pandurangan

• Malavika Avinash - Judge

• Charles Vinoth - MLA

• Shanmugarajan 

• Sugunthan 

• Vishalini 

• Vittal Rao 

• Subhashini 

• Baby Monika Siva 

• Thavasi Raj 

• Rajee Vijay Sarathy - Mrs. Venkatesh

• Abhirami 

• Ananya 

• Santhosh 

• Vaishali 

• Osthi Ramu 

• Besant Ravi - special appearance

• Dinesh special appearance 

• Thangamani Prabhu - Medical College Investigation Officer

Waƙoƙin Shirin 


1. "Pattaya Kelappu" 
2. "Nilaayo" Vairamuthu 
3. "Pa Pa" 
4. "Azhagiya Soodana Poovey" 
5. "Varlaam Vaarlam Vaa Bairavaa" 
 
©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)