YABO
Bincike ya nuna cewa: 'Dabbar da ake yaba mata a fili yayin da ta yi abin kirki ta fi saurin fahimtar abu ta kuma adana abin a ƙwaƙwalwarta fiye da wadda ake duka da kora idan ta yi kuskure'. Binciken ya nuna su ma mutane hakan na faruwa da su. Haka kuma wani mai hikima ya taɓa cewa; "kamar yadda kowa ba ya so ya ji an kushe shi, haka kowa ke so ya ji an yabe shi." Kenan, waɗannan maganganu kaɗai sun isa su bayyana maka irin muhimmancin da yabo yake da shi a rayuwarmu ta yau da kullum.
Hausawa kan ce 'yaba kyauta, tukwici.' Mafi ƙarancin tukwicin da za mu iya bayarwa idan an yi mana abin arziƙi shi ne mu godewa wannan mutumin kuma mu yaba masa bisa ƙoƙarin da yayi. Amma mutanen wannan zamani sam wannan abu bai dame mu ba. Matan aure da dama su kan ƙullaci mazajensu a rai saboda ƙarancin samun yabawa ƙoƙarin da suke yi a harkar zamantakewar aure wanda kuma hakan sam bai dace ba. Domin wata sai ta shekara biyar tana yin wani abin kirkin mijin bai taɓa gode mata ba balle ya yaba, amma rana ɗaya in ta yi kuskure sai ya hauta da zagi, don Allah me zai sa ba za a dinga samun matsala a zaman aure ba?
Haka nan su ma wasu matan, miji zai fita, Allah kaɗai ya san irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya samu abin da ya kawo gidan, amma abu na farko da za ta yi ƙorafi ne na ina kaza? Naga baka siyo kaza ba, bayan kuma na faɗa maka ba mu da shi. Fisabilillah ta yaya ba za a dinga samun matsala ba? Iyayenmu su ma suna da nasu, ko da yake haƙƙi ne akan kowane ɗa ya yi wa iyayensa biyayya tare da taimakonsu da duk buƙatun yau da kullum, amma fa daɗin da zai ji na musamman ne idan aka yaba masa bisa ƙoƙarin da yake yi.
Wani abun jin daɗi kuma shi ne; shi fa yabon nan in ka yi shi ba wani abu zai rage ka da shi ba, hasali ma sai dai ya ƙare ka. Wa Ma'aurata, ku gwada wannan misalin da zan ambata ku ga irin sauyin da za a samu. Wa mai gida, ka gwada yabon girkin matarka da yabo na tsakani da Allah har cikin ranka ka ga yadda goshinta zai dinga ƙyalli, fuskarta tana sheƙi cike da annuri saboda jin daɗin ka yabe ta. Sannan ka tsumayi girkin da za ta maka na gaba ka gani. To daga nan ne za ka fahimci irin sauyin da za a samu in da ace kullum za ka ke yaba mata. To amma matsalar mu ba mu iya haka ba, kullum sai dai ƙorafi.
Ɗan uwana, ba fa cewa nake yi ka zuga mutum ba, a'a ko kaɗan. Abin da nake nufi shi ne ka nuna wa mutum jin daɗin ka a fili idan ya faranta maka rai. Haka idan mutum ya yi wani abun kirki ka nuna farin cikin ka a fili. Hakan zai faranta masa rai kuma kai ma ya faranta maka. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, zai ƙara wa wanda aka yi wa ƙwarin gwiwa, zai kuma gyara zamantakewar da ke tsakaninku. Wannan shi ne abinda nake nufi. Mamana, yaronki ne ya fito zai tafi makaranta, tsayar da shi ki yabi kwalliyar da ya yi, ki yaba ƙoƙarinsa kuma ki sa masa albarka sannan ki bi shi da addu'a, in sha Allah yaran nan karatun da zai ɗauka a ranar na musamman ne. Amma kin bishi da zagi ya tafi makarantar da fushinki, fisabilillah ta yaya zai iya fahimtar karatun? Hakanan in ya dawo ki yaba wa ƙoƙarin da yayi kafin ki yi ƙorafi akan abin da ya yi na kuskure.
Wato a ko da yaushe, a shirye mutane suke da su karɓi duk gyaran da za ka yi musu na kuskure matuƙar da fari ka yaba musu akan ƙoƙarin da suka yi. Amma mafi yawancin mutane mun fi sabawa da ƙorafi tukun kafin in ma za mu yaba ɗin sai mu yaba daga baya, bayan mun ɓata wa mutumin rai. Kuma daga nan ba lallai bane ya saurare mu, saboda zuciyarsa ta sosu kuma gwiwarsa ta riga ta yi sanyi.
Kushe, ƙorafi da rashin yabawa shi yasa da yawan ɗalibai ba sa maida hankali wajen karatu. Kamar yadda da yawa hakan ke jawo mace-macen aure ko rugujewar alaƙa. Wani zai iya cewa, to in kuma ban ga abinda zan yabi mutum a tattare da shi fa? Sai in yi ƙarya? Haba bawan Allah? Ta yaya za a ce mutum ba shi da wani abu da za ka iya gani a tattare da shi da ya cancanta a yabe shi da shi? Ai ko shaiɗan yana da abin yabo, domin kuwa yana da ilimi sai dai ace bai yi masa amfani ba tun da ya yi girman kai, amma ba a ce ba shi da shi ba.
Sannan yabo kowa na iya yinsa ga kowa. Iyaye da 'ya'yansu, mata a miji, saurayi da budurwa, maƙwabci da maƙwabci haka dai gasu nan. A kowace mu'amala da muke yi za mu iya shigar da wannan ɗabi'a. Abokinka ne ya yi maka wani abu misali sai ka ce masa 'wane nagode sosai, Allah ya saka da alheri, haƙika ka taimake ni sosai kuma na ji daɗin hakan, tabbas kai aboki ne nagari, Allah ya bar zumunci'. Tsakani da Allah ko kai aka faɗa wa haka ba za ka ji daɗi ba? To me zai sa mu bari ƙunci ya shiga ranmu bayan muna iya kawo sauyi a hankali? Ko yaro ka aika in ka gode masa kuma ka yabe shi sai ka ga alamun jin daɗi a tare da shi na musamman.
A taƙaice dai 'yan uwana, saƙon da nake son isarwa shi ne mu rage yawan ƙorafi da kushe ƙoƙarin junanmu, mu rungumi godiya da yabon ƙoƙarin junanmu, hakan shi zai kawo mana ci gaba mai ɗorewa a zamantakewar mu in sha Allah.
Allah ya azurta mu da kyakkywar fahimta amin.
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com