SHARHIN FIM ƊIN VINAYA VIDHEYA RAMA


SHARHIN FIM ƊIN VINAYA VIDHEYA RAMA 

Vinaya Vidheya Rama fim ɗin India ne da aka fitar da shi cikin harshen Telugu a shekara ta 2019. Fim ne na faɗa, barkwanci da kuma zamantakewa. An fassara wannan fim a cikin harshen Hausa in da aka sa masa suna Uwarwatsi. Duk da cewa fim ɗin ya yi kyau sosai, bai taka irin rawar da aka yi tunanin zai taka ba ta harkar kasuwanci. 

• Bada Umurni - Boyapati Srinu

• Ɗaukar Nauyi - DVV Danayya

• Labari/Tsarawa - Boyapati Srinu

• Taken Shiri - Devi Sri Prasad

• Horaswa - Rishi Punjabi & Arthur A. Wilson

• Tacewa - Kotagiri Venkateswara Rao & Thammiraju

• Kamfanin Da Ya Shirya - DVV Entertainment

• Ranar Fita - 11 January 2019

• Tsayin Shiri - Mintuna 146 

• Ƙasa - India 

• Harshe - Telugu

• Kasafi - ₹70 crore

• Kasuwancin Box Office - ₹95 crore


LABARIN SHIRIN A TAƘAICE. 

Labarin ya fara ne da nuno wasu yara marayu kuma mabarata a filin jirgin ƙasa a lokacin da suka ka ana satar yara, da aka gane su sai suka yanke shawarar su kashe kansu saboda tsoron za a kashe su. A yayin da suka tunkari jirgin ƙasa domin su mutu, sai suka ji kukan jariri a wani surƙuƙi da ke kusa da su. Ko da suka lalubo in da jaririn yake, sai suka ga ashe jinnaku duk sun cije shi a jiki, hakan ya sa suka kai shi asibiti mafi kusa. Bayan jaririn ya samu sauƙi, sai suka yanke shawarar su raine shi a matsayin ƙaninsu. Daga nan sai suka sa masa suna Ram, kuma suka sa shi a makaranta. 

 Ashe mai satar yaran nan shi kuma ya fito daga gidan kaso, don haka sai ya zo inda suke da nufin halaka su, amma sai Ram ya caka mai wuƙa ya ceci rayuwar 'yan uwansa. Da likitan da ke kula da su ya tambaye shi, sai ya ce ya tura 'yan uwansa makaranta shi kuma zai yi aiki a madadin su. A haka dai wannan likita ya raine su duka a matsayin 'ya'yansa. 

Daga nan kuma sai labarin ya dawo da mu izuwa yanzu, in da aka nuno Ram Konidela ya kashe wani ƙasurgumin ɗan daba da ke Bihar mai suna Raja Bhai Munna, amma ashe mafarki yake yi. Ahalinsa ya ƙunshi 'yan uwa maza ne guda huɗu, matansu guda huɗu, mariƙinsu da kuma yaransu.

Ɗaya daga cikinsu wanda ake kira Bhuvan Kumar kwamishinan zaɓe ne, kuma sauran 'yan uwan nasa guda uku suna aiki ne tare da shi. Shi kuma Ram an yi baikonsa da Sita, ɗiya a wajen wata mai kare haƙƙin mata da ake kira da Puppy. Wani ƙaramin ɗan daba da ke son ganin ya ci zaɓe mai suna Ballem Balaram ya yi ƙoƙarin ba wa Bhuvan Kumar cin hanci bayan ya ƙwamushe masa mota cike da kuɗi. Yayin da Bhuvan ya ƙi amincewa, sai ya yi masa barazana. Hakan yasa Ram ya bashi kashi a gaban 'yan jarida. Wani surukin Balram mai suna 
 Pandem Parasuram sai ya ƙalubalanci Bhuvan tare da cewa ya bada haƙuri, amma Ram sai ya nuna masa tsageranci. Hakan ya sa ya ji babu daɗi. Don haka sai ya haɗa baki da wani gurɓataccen Ɗan Sanda ya je gidan su Ram ya ɗauke ahalinsu baki ɗaya. Ram sai ya isa inda suke kuma ya ba Parasuram haƙuri. Ana cikin haka ne kuma sai ga 'yan daba daga Bihar waɗanda Raja Bhai ya turo. Bayan ya yi faɗa da su, sai Surikarsa wato Gayatri ta ke tambayar Ram dalili. To anan ne aka fara nuno mana abinda ya faru a baya. 

 Raja Bhai wani ɗan mulkin mallaka ne da ke zaune a Bihar, kuma har ma ya yi barazana wa babban Minista. Hakan yasa babban Minista ya roƙi gwamnati ta tsakiya da a bashi Bhuvan a matsayin shugaban zaɓe na jahar Bihar. Raja Bhai sai ya kama Bhuvan tare da sauran abokan aikinsa. Hakan ya sa Bhuvan ya kira Ram wanda a wannan lokaci yana Gujarat tare da ahalinsa. Cikin sauri Ram ya bar tashar jirgin saman da yake ya nufo inda Bhuvan yake. Sai da ya kashe mutum 300 shi kaɗai akan doki kafin a kama shi a kai shi wajen Raja Bhai. 

A nan dai faɗa ya ɓarke in da Raja Bhai ya kashe Bhuvan yayin da shi kuma Ram ya yi masa mummunan rauni wanda ya barshi a kwance. Gayatri ta yi matuƙar kaɗuwa da jin wannan labari na mutuwar mijinta. Daga nan sai ta roƙi Ram da ya nuna mata in da aka ƙona Bhuvan, daga nan kuma sai ta roƙeshi ya kai ta inda Raja Bhai yake, a nan ne ta ƙalubalanci raja da ya yi faɗa da Ram. A taƙaice dai Ram ya kashe Raja Bhai daga baya kuma suka koma gida shi da ahalinsa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Post a Comment (0)