RUBUTACCIYAR WAƘAR GUGAN ƘARFE


WAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA 


Gugan Ƙarfe

Masu fagabniya a gari
Jure kwaramniya bidiri
Balle ma ta taƙadari
Ɗanduƙusuru mai bidiri
Masu kamar yabo a gari
Ga su kamar suna zikiri
Baƙin halinsu ƙona gari
Ya sattaru Al-ƙadiri
Tsare mu baƙin shirin ja'iri
Kamar na ashana ƙona gari.

Jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari, Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari.

A yau ƙoƙon bara na taho gurin mai juya al'amari
Kashe mani gobarar kogi da ta fi ta zahiri bidiri
Wuta daga bahari kogi kasan da akwai shirin garari
Idan ka tsaya mani wuturi
To bani shirin ganin bidiri.

Muhammadu sahibul bushra da ke horo da ai haƙuri
Naziru na gargaɗin da kake da ribar masu yin haƙuri
Muna roƙon gwani wuturi
Ya ƙara dubu-dubun zikiri
Gurin Musbahu cinye-gari
Muhammadu sahibul bashari.

Akwai su gwani akwai nagwanaye akwai agwanaye duk a gari
Akwai 'yan bani ni na iya akwai 'yan mu muke a gari
Akwai 'yan mu da mu aka fara sannan mu muke da gari
Akwai 'yan mu muke fa da gado ba mu bari a karɓi gari.

Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari, jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari.

Akwai 'yan ba mu sha kuma ba mu bari wasu ma su sha a gari
Su jaɓa da an sako baki a yau kwalara ta watsu gari
Da masu shirin gada ta zare suna tarko na mai haɗari
Da an kai walƙiya sun zam kamar sun sha ruwan tsari.

Suna da faran-faran a kama suna da wutsilniyar badari
Ga zulwajahaini guntsi-baza kullum aikinsa zaga gari
Yana hana mai zuma talla, yana tallar maɗi a gari
Gari ya watstsake kure yana kiwo tsaka ta gari.

Akwai su ƙuda mazan kwaɗayi halak da raham yana marari
Da yaki-halak da yaki-haram yake burga kamar mazari
Ina ranar sanin ilimi na hauni da dama ai nazari
Kamar jaki da littattafai cikin akumare ba nazari.

Akwai su biri uban ɓarna gata a birai fa taƙadari
Akwai su dila uban wayo da sari ka noƙe ba tare
Akwai kura da kan rago cikin babbansu al'amari
Umurun almushtabiha sai dai dafa'i na yin zikiri.

Akwai riga ta malanta da kan sawa a zare kwari
Da kambun baki al'ainu da yasan ƙage duk sihiri
Hawayena a kunduƙuƙi ina roƙonka Al-ƙadiri
Tsare mu balahirar maƙiya mayar masu dukkanin ƙuduri.

Waɗansu wutar ciki tamkar an bai maye riƙon jinjiri 
Waɗansu ko handama tamkar loma aka bai wa almajiri 
Suna hannu-baka-hannu-ƙwarya tamkar su cinye gari 
Idon su da kunnuwa a rufe summum-buƙumum cikin garari. 

Jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari, Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari.
Post a Comment (0)