TUNATARWA GAME DA SALLAMA


_*Darasinmu na yau, hadisin da ke da ala'ka da sallama*
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce; {MUTANE GUDA UKU ALLAAH YA LAMUNCE MUSU, IDAN SUN RAYU ALLAAH ZAI AZURTA SU KUMA YA ISAR MUSU, IDAN KUMA SUN MUTU ZAI SHIGAR DA SU ALJANNA (SUNE); WANDA YA SHIGA GIDANSA SAI YAYI SALLAMA, WANDA YA FITA ZUWA MASALLACI, DA WANDA YA FITA ZUWA 'DAUKAKA KALMAR ALLAAH.}*_

```[Sahihut Targib;321,Haakim;2400,Jamiul Ahadith;11236,Abu Dawud;2494,Ibn Hibban;499]```
*Wannan hadisin yana nuna mana cewa duk wanda ya kasance cikin mutane ukun nan toh zai samu lamuncewar Allaah da kuma tsarinSa. Allaahu aalam.*
Post a Comment (0)