KISSAR WANI MUTUM DA YA SABA MA ALLAH SHEKARU 40

KISSAR WANI MUTUM DA YA SABA MA ALLAH SHEKARU 40:



An ruwaito cewa zamanin Annabi Musa, Alaihis salam, fari (rashin ruwan sama) ya samu Bani Isra'ila, sai suka taru su dubu saba'in ko fiye da haka suka je wurin Annabi Musa, suka ce: Ya wanda Allah ya yi magana da shi, ka roka mana Allah Ya shayar da mu ruwan sama. Sai Annabi Musa ya tashi ya fita tare da su zuwa filin da ke wajen gari. 

Daga nan Annabi Musa Alaihis salaam, ya ce: "Ya Ubangiji ka shayar da mu ruwan sama, Ka yada RahamarKa a gare mu, Ka tausaya mana saboda dabbobi da kananan Yara da suke cikin mu da tsofaffi... 

Annabi Musa Alaihis salaam ya ci gaba da cewa:" Yaa Allah kar ka haramta alherin da ke wurin Ka, saboda laifinmu". 

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa a cikinku akwai wani bawa shekara arba'in yana saba mun, ku umurce shi ya fita daga cikinku, domin saboda shi na hana ku ruwa". 

Sai Annabi Musa ya ce: "Yaa Allah ni mutum ne mai rauni, kuma muryata ba za ta isa ba saboda yawan su ya kai dubu saba'in ko fiye da haka. Sai Allah ya ce da shi kai dai ka yi kira ni ne mai ikon isarwa. 

Sai Annabi Musa ya juya yana kira cikin mutane yana cewa: Ya kai wanda ka yi shekaru arba'in kana saba ma Allah, ka fita daga cikinmu, domin saboda kai aka hana mu ruwan sama.

Lokacin da wannan bawa ya duba hagu da daman shi bai ga wanda ya fita ba sai ya fahimci lallai shi ake nufi, sai ya fadi a cikin zuciyar shi: idan na fita a cikin wadannan mutane shi ke nan asirina ya tonu; kuma idan na zauna za a hana su ruwan sama. Sai ya shigar da kansa cikin rigar shi yana mai nadama akan munanan ayyukansa yana cewa: Yaa Allah na saba maka tsawon shekara 40 amma ka yi mun jinkiri ba ka kama ni ba, to yanzu gani na zo maka a matsayin mai da'a don haka Yaa Allah ka karbe ni. Wannan bawan Allah bai gama magana ba sai ga sama ta hada hadari kuma Allah Ta'ala Ya saukar da ruwa. 

Sai Annabi Musa Alaihis salaam ya ce: "Yaa Allah ga shi Ka shayar da mu alhalin babu wanda ya fita daga cikinmu". 

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa na shayar da ku ne saboda bawan da ya hana ni in shayar da ku, domin ya tuba ya dawo gare ni. 

Sai Annabi Musa ya ce:" Yaa Allah ka nuna mun wannan bawa mai da'a kuma mai tuba?".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Ban tozarta shi ba alhalin yana saba mun sai yanzu da ya tuba zan tozarta shi?".

Domin ganin inda na ciro kissar za a iya duba littafin قصص التائبين na فضيلة الشيخ محمود المصري. 

Allah Ta'ala Ya ba mu ikon tuba daga zunubanmu kuma Ya gafarta mana. 

Dan uwanku a Musulunci: 
Sheikh Umar Shehu Zaria
Post a Comment (0)