HUKUNCIN YI WA KARUWAI GYARAN JIKI


*HUKUNCIN YI WA KARUWAI GYARAN JIKI*

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

 *TAMBAYA:* ❓

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu, malam don Allah ina da tambaya, mace ce ke sana'an lalle da kitso da gyaran jiki shin ya halatta ta yi ma karuwai? na gode Allah ya kara basira.

 *AMSA* :👇

Wa'alaikumus Salamu wa Rahmatullah wa Barakátuhu, Allah Maɗaukakin Sarki a cikin Alqur'ani mai girma ya yi umurni da mu yi taimakekeniya a wurin aikin kirki da tsoron Allah, kuma ya hana mu yin taimakekeniya a wurin saɓo da qetare iyaka (zalunci) a aya ta 2 da ke Suratul Má'ida.

Gyara wa maÉ“arnata hanyar yin É“arna da qara qawata abin da ake É“arnar da shi, yin hakan ma É“arna ce, su karuwai suna yin amfani da jikinsu ne wurin aikata alfasha tare da kwastamominsu maÉ“arnata, to bisa dogaro da waccan ayar ta Suratul Má'ida da Allah ya hana yin taimakekeniya wurin saÉ“o, sai ya zama bai halasta mai sana'ar gyaran jiki ta riqa gyarawa karuwai jikinsu ba, musamman idan ya kasance abin da take gyarawar yana taimaka wa muguwar sana'arsu ta karuwanci, saboda yi masu gyaran jiki taimaka masu ne wajen su yi kasuwa. 

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)