HUKUNCIN YIN ADDU'A BAYAN SALLAH


*HUKUNCIN YIN ADDU’A BAYAN SALLAH* 

https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm

*TAMBAYA*❓

Assalama alaikum
Malam mutum ya shigo masallaci sai tarar da jam i har guda biyu a cikin masallacin toh ya ya kamata yayi wajen bin sallah

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Allah yana cewa acikin suratul bakara aya (186)
 *ujiybu da’awatud daaiy iza da’aan*
"ina amsa rokon mai roko yayin daya rokeni”.
wannan ba wani lokaci da Allah ya ware yace bandashi.
Ya dan uwa: musulmi yana da lokuta muhimmai da Allah(S.a.w)yake amsa addu’arsa musamman in ya idar da sallar farillah.Abinda zai tabbatar maka da haka shine fadin Allah (s.w.t)
 *fa’iza faragata fansab,wa ilaa rabbika fargab* 
”idan ka idar da “sallarh”ka kafu kayi kwadayi izuwa ubangijinka”
suratul sharhi aya ta(7-8).
Malaman tafsiri sun fassara wannan aya da ma’ana biyar amma kunzumin malamai sun tafi akan cewa ma’anar wannan aya shine ( *faiza faragata minas salati fansub lid duaa’i* )”idan ka idar da sallah ka kafu kaita addu’a”.
Manya manyan sahabbai kamar ibn abbas da tabi’ai kamar dhahhaku da mukatilu da mujahidu sun fassara wannan ayar da wannan ma’ana,malaman tafsiri kuwa da suka fassara wannan ayar da wannan ma’ana akwai:- imamul mufassirina (addabari)juz’I na 12 shafi na 760,faharaddinir raazi akicin “mafatiyhul gaib”juz’I na 32 shafi na 8,ibn kasiyr acikin “tafsirul kur’an”juzu’I na 4 shafi na 530.khur dabiy juz’I na 20 shafi na 74, dabriysi acikin “mujma’ul bayaan’shi kuwa cewa yayi:-wannan shine ra’ayin yayan Annabi(s.a.w) yace ma’anarsa *(faizaa faragata minas salaatil maktuubati fansub ilaa rabbika bid du’aai wa ragaba ilaihi fil mas’alati yu’udika)* ”idan ka idar da sallar farilla ka kafu izuwa uban gijinka da addua kai kwadayi gareshi cikin roko zai baka “
sannan annabi(s.a.w)yana cewa:( *izaa sallah ahadakum fal yabda bi tah miydullahi ta’aalah,wassanaai alaihi,summa yusalli alannabiyyi,sallallahu alaihi wasallama,summa yad uw bima shaa’a* )
”idan dayanku yayi sallah ya fara da godiya ga Allah,sannan yayi masa kirari sannan yayiwa Annabi (S.A.W)salati sannan yayi roko da abinda yaso.Amma wasu gwanayen kauce kauce sukance ba addu’ar suke musawaba a’a jam’inta suke musawa.ta shima jam’in addu’ar bayan sallar ga dalilinsa daga Allah(swt)da Annabi (s.a.w)Allah yana cewa( *ya bunayya akimis salaata wa’amur bil ma’aruufi* )surah lukman aya 17”ya dana ka tsaida sallah kayi umarni da kyakyawa”a harshen lukman. To ashe idan liman yace a karanta i.fatiha ii.salatul faith iii.istigfari ai aiki yayi da wannan umarni guda biyu na wannan ayar da hadisin daya gabata.
Umarnin Annabi (s.a.w)kuwa 1 imamu ahmad ya ruwaito a musnad jizi’I na 16 shafi na 246.2.turmuzi a “sunan”juz’I na 2 shafi na 254.3. ibn aby shaiba a “musannaf’ juz’I na 2 shafi na 267.4.Abu dawd a” sunanu”´jiz’I na dayA shafi na 110.5.Baihaki a “sunanu” jiz’I na uku shafi na 408, 
Annabi (S.AW)yace:( *laa ya’atiy ahadukumus salaata wahuwa haakinun,walaa yu’umanu ahaduku fayakhassa nafsahu bid du’aa’I duunaahum,faman fa’ala fakad khanahum* 
””kada dayanku ya jewa sallah yana mai matse kari,kuma kada yayi limanci ya kebanci kansa da addu’a banda mamu.Wanda duk ya aikata haka to ya ha’incesu”.
Daya ruwayar kuma yana cewa:” *man kaana yash hadu anni rasulullahi fala yash hadus salaata hakinun hatta yata haf fafa,waman kana yash hadu anniy rasulullahi fa amma kauman falaa yakh tassu nafsahu bid du’a’i….”* 
.”duk wanda ya shaida ni Manzon Allah ne to kada ya halarci sallah yana matse kari,duk wanda ya shaida ni manzon Allah ne ya limanci mutane to kada ya kebanci kansa da addu’a….”.To wannan shi ne sakon da Manzon Allah (s.a.w)yake bawa limamai.don haka duk wanda zaice addu’ar Liman bayan sallah ba kyau to shine zai kawo nassi,kamar yadda muka kawo.Duk da masu musa wannan maganar suna cewa wai a cikin sallah Annabi(s.a.w)yake nufi sun manta duk addu’ar da Annabi(s.a.w)yake yi acikin sallah kansa kadai yake yiwa baya sa kowa aciki.Allah ya kiyaye Annabi(s.a.w)yayi umarni da Alkhairi shi kuma ya ki aikatawa.

Wallahu A'alam

*aaz
Post a Comment (0)