MIJI ME TSORON MATARSA


*MIJI MAI TSORON MATARSA* 

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA* ❓

Assalamualaikum malam antashi lfy ya Kukari damu munakara godeya gareka akan akan taimakun da kake yimuna da addu'u Allah ya saka da akhaira ya kara nisan kwana ameeen ya Allah"

Mlm dan Allah inason kabani shawara wanine takesona da aure amma naga kamar Yana tsoron matarsa kokuma baya son bacin ranta komai dai kamar tafi karfinsa toh dama can inada yara guda 4 kuma inada gidana amma mlm nafison duk wada zan aura inje gidansa koda kuwa baikai nawa ba shine yanzu yace min adaura aure koda matarsa bata sani ba wai daga baya zata hakuru sai inzauna gidana kuma ita matarsa yarinya guda garesu wlh mlm inason shi shima Yana sona amma ina gudun matsala da zata biyu baya sabida nasha wahala baya gidan aurena dan Allah mlm kabani shawara yazan fitoma wannan lamari ngd sosai Allah ya saka da alhere.


 *AMSA* 👇

A tawa shawarar Kar ki Auri Mutumin da yake Jin Tsoron Matarsa ta Gida. Alhalin ke ki je ki same ta a Matsayin Kishiyar ta.
 Na sha bada wannan shawarar Akan Cewar ko da ya Aure ki. Sai Abinda Wannan Matar ta ce Akansa ko Akanki Za'a yi. Shine ake cewa MIJIN TA CE. Wai Mai Tsoron Matarsa, Sai Abinda ta Ce Masa Zaiyi. Wanda Irin Wadannan Mazan Su Kan fifita Umarnin Matan su Sama da ta Kowa, Hatta Akan Ta Iyayensu.
 Kinga Kuma Indai har ta kai ga Macen da Za'a ce Mijinta yana Jin Tsoron ta. To fa ba a Banza ba. Ko dai hakan yana Faruwa ne Ta Hanyar Sihiri da Asiri ko Kuma da Masifar ta ne ya sa yake Jin Taoron ta. Ma'ana Bala'in yau da bala'i na Gobe da ban. Sabida Shine Cinyewar Mace Ace Mijinta yana Jin Tsoron ta. Idan ya so idan ta je Lahira Allah yayi Mata duk Abinda ya so na Nau'in Azaba. Ita dai burinta ya Cika a gidan duniya. A lahira Kuma Ko Menene Ma Ayi Mata ta Amince da Hakan.
 Allah ya sawwake.
 Kuma Irin Wadannan Mazan Akasarin su, Zakiga Allah yana Takaita Rayuwar su. Ma'ana sunfi Mutuwa da Wuri, Domin Saukar da Jarrabawa ga wannan Matar. Ko kuma ita Allah ya gajarce Mata Rayuwar ta, ta Mutu ta bar Duniyar, don shima ya dandani dadin Rayuwar Wannan Duniyar.
 Gashi Kuma Kince Kin sha Wahala a gidan ki na Baya, idan Kuka Auri Wannan da yake Tsoron Matarsa din. Na Tabbatar Miki da Cewar a haka nan ma zaki sha Wahala. Ba Mamaki ke a haka Kaddararki ya zo kenan. Har ki bar Wannan Duniyar.
 Domin Wallahi irin Wadannan Matan sukan hana Miji zuwa gidan Kishiya da kwana ko da Wuni.
 Akwai wanda na sani. Wallahi bai isa ya je Gidan Uwar gidan sa da sunan Wai zi kwana ba. Sai dai ya je su yi shirar dare. Alhalin kuma ita aka zo aka tarar a gidan ta da Mijinta. Amma hakan ta Kasance. An Rabata da Mijinta. Bai isa ya zo Gidanta ya kwana ba. 
  Kinga da muguwar Rawa Gwanda Kin Tashi.
 Ki Hakura ki Ci gaba da Addu'ar Allah ya kawo Miki Wanda zai Tausaya miki ya Ji Kanki. Wanda ya fi Karfin Gidansa. Ba wanda Gidansa ya fi Karfin sa ba.
 Ki yi Hakuri Ki Ci gaba da Addu'a Akan Allah ya kawo Miki Namiji Jajirtacce wanda ya fi Karfin Gidansa.

Allah Shine Masani.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)