MIJINA MAZINACI NE


*MIJI-NA MAZINACI NE* 

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum, mallam mijina ya kasance mazinaci kuma ni na tabbatar da hakan kamar yadda sharia ta tanadar, kuma har magani mun karba a asibiti sakamakon cututtukan dake samuwa sakamakon haka, nayi hakuri ganin bai rageni da komai ba. Nayi tayi masa addu'a shekaru da dama amma ba wani canji, kuma yanzu baya ma kusanta ta.
Mallam meye abinyi a shari'ance?


*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Abinda ya kamata shine ki sanar da magabatanku. Domin kuwa wannan bayanin da kikayi, ba Qaramin abu bane.
Allah (SWT) ya hana aure atsakanin Mazinacin miji da kuma Mace mumina wacce batta Zina. Acikin suratun Nuur ayah ta 3 yana cewa:
"MAZINACI BA ZAI AURA BA SAI DAI MAZINACIYA KO MUSHRIKA. HAKANAN MAZINACIYA Ba ZATA AURA BA SAI DAI MAZINACI KO MUSHRIKI. KUMA AN HARAMTA WANNAN ABISA MUMINAI"
Malaman tafseeri suna kafa hujjah da wannan ayar cewar aure atsakanin mazinata da muminai bai halatta ba.
Kuma akwai hatsari mai yawa agareki cikin zama da wannan bawan Allah. Domin kuwa watarana zai iya zuwa ya kwaso miki H.I.V AIDS ko kuma wata chutar mai wahalar magani.
Sannan kuma kowacce mace burinta shine Uban 'ya'yanta ya zamto mai kyawun halaye Da tarbiyya yadda zai zama abin alfahari awajen 'Ya'yansa.
Amma ya kamata lallai ki zauna tare da waliyyan aurenki ki bayyana musu halin da kike ciki sannan su kuma su tunkareshi ko manyansa, sannan ayi masa nasiha. Idan ya yarda ya tuba ya chanja halayensa, to shikenan.
Amma idan yaqi yarda, ko yayi tawaye, to mafi alkhairi agareki shine araba auren.
Idan ba haka ba, zai iya sanya kema ki kauce hanya idan ba Allah ne ya kiyaye ba.
WALLAHU A'ALAM

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)