KA KYAUTATA ALAƘARKA
.
Ka zama mutum mai sauƙin kai da faɗin ƙirji; mai haƙuri da kawar da kai daga ababan da aka yi masa na baƙanta rai, domin kuwa babu ƙarfi ga mai saurin kaye, sai dai ƙarfi na ga mai iya danne fushinsa idan aka yi masa abin da ya baƙanta masa rai.
.
Da ɗai kada ka yarda ka biyewa mai nemanka da rigima ko faɗa, idan ya faɗa maka zance marar daɗi kai ka faɗa masa mai daɗi, domin kuwa hakan ɗaya ce daga cikin siffofin bayin Allah mai rahma, Allan ya kira su da "Bayin Allah mai rahama" saboda zai yi musu rahamar ne. Watau su idan jahilai suka zage su ko suka cutar da su da zantukansu ko aikinsu sai su ce a zauna lafiya. Abin nufi su da aka yi wa laifin su ke neman sulhu ba wai don ba su da ƙarfin ramawa ba ne, sai don biyayya ga Allah.
.
Siffantuwa da kyawun hali zai sa a duk lokacin da aka tashi ambatonka ko da bayan babu ranka ne a ambace ka da alheri, don haka rayuwar Manzon Allah SAW ta zama abar kwaikwayo a gare ka ya kai bawan Allah. Ka kula da duk wani aiki da za ka aikata, kada ka aikata shi don neman suna ko yabon mutane ƴan uwanka. Lallai su mutane ba a birge su, amma idan ka yi don Allah shi kaɗai sai ya karɓa, kuma ya saka maka da mafi kyawun sakamako (aljannah).