HUKUNCIN YIN AMFANI DA MAGANIN MATA

*HUKUNCIN YIN AMFANI DA MAGANIN MATA :* 

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

*TAMBAYA*❓

Aslm Alagafarta malan Dan Allah tambaya nakeyi gameda amfani da maganin Mata ga me kishiya.
Wasu sunce haramun ne mace daya tayi amfani dashi sedai in zasu hada kansu suyi gaba daya. wasu kuma sunce a'a ko wacce tanada ikon yin abunta Dan ta kwaci kanta ita daya Dan Allah malan wanne ne gaskiya?

*AMSA*πŸ‘‡

Wa alaikis salam.

Idan na fahimci tambayarki kina nufin irin maganin da mata ke amfani dasu domin mallakar hankalin mazajensu.

To su dai magungunan mata kashi biyu ne kamar haka :
1. Akwai wadanda suke amfani da wasu saiwoyi ko kayan abinci na musamman domin samarwa jikkunansu kyawu da tsafta yadda zasu Qara gamsar da mazajensu fiye da yadda da suke.
Wannan halal ne mutukar ba'a sanya najasa ko wani abun tsafi ko sihiri ko chamfi acikinsa ba.

2. Akwai wadanda suke amfani da wasu abubuwa na chamfi ko tsafi su goga ajikinsu, ko su sanya acikin gabansu, ko su sanya ma mazajensu acikin abincinsu domin mallakar miji ko dukiyarsa. Wannan gaba dayansa haramun ne saboda abubuwan dake cikinsa na tsafi ga kuma cutarwa ga mazajen.
Kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "BA YA CIKINMU DUK WANDA YAJE CHAMFI KO KUMA AKAYI MASA CHAMFI, KO YAYI BOKANCI KO AKAYI MASA BOKANCI. KO YAYI TSAFI KO AKAYI MASA TSAFI DOMINSA. DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KUMA YA YARDA DA ABINDA YA GAYA MASA, TO YA KAFIRCE WA ABINDA AKA SAUKAR WA ANNABI MUHAMMAD (SAWW)".
(Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi da isnadu mai kyawu).

Don haka duk wacce taje wajen boka aka bata wani abu tayi amfani dashi ko kuma ta sayar wa wadansu matan sukayi amfani dashi, to tabbas gaba dayansu laifin ya shafesu (wato kafirci kamar yadda hadisin ya bayyana).
Mata kuji tsoron Allah ku fahimci cewa samun mallakar zuciyar miji ta hanyar amfani da layoyi ko kulle-kullen tsafi ba samun yardar Allah bane. Hasali ma hanya ce ta kafirci da gushewar imani. Amma zaku iya samun mallakar mazajenku ta hanyar ladabi da biyayya da girmama miji tare da gyaran jiki da kyautata halaye.
WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyarπŸ‘‡
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on FacebookπŸ–•

Post a Comment (0)