MU YI NAZARI


Mai fushi da mai dariya, mai murna da mai kuka, duk baza su hana duniya tafiya ba. Hutar da rayuwarka kada kasa damuwa ta hana rayuwarka ci gaba.
°
Kada ka yi gadara da kyan fuskarka domin ba kai ne ka yi ta ba. Kada ka yi kuri da asalinka domin ba da shawararka aka haife ka a gidanku ba. Yi alfahari da zama mutumin kirki wannan shi ne abinda ka aikata.
°
Lema bata hana saukar ruwan sama amma tana sassauta wahalarsa, idan baka iya kawar da matsalar dan uwanka, to ka zamo masa lema mai rage masa damuwa.
°
Ka daina kallon laififfikan mutane kamar kai ubangiji ne kai baka laifi Dukkanmu muna cikin rufin asirin Allah ne, in da Allah zai bude hijabi da ka raina kanka.
°
Duk wanda ka hadu da shi akwai rawar da zai iya takawa a rayuwarka. Wani zai taimake ka, wani ya nemi taimakonka, wani ya so ka, wani ka so shi, wani ya amfane ka,wani kuma kai ka amfane shi.
°
Agogo yana zagayawa ne a kan kowace sa'a. Haka rayuwa take zagayawa da mu a kan yanayi daban daban. Yi haquri idan yanayinka a yau bai yi dadi ba, wataqila gobe ne za kayi dariya.
°
Idan ka saki hawayenka a kan filo ka sake su a banza. Tashi ka kwarara su a tabarmar sallarka. Idan ka yi haka, ka kai qara wurin mai share maka su.
________________________
Allah yasa mu dace duniya da lahira.
Post a Comment (0)