GOOGLE TRANSLATOR



ASOF_2021 KANO CHAPTER 


KO KANA DA MASANIYA AKAN GOOGLE ONLINE TRANSLATOR ?


    Kai tsaye ba komai ake nufi da google online translator ba face kawai wata manhaja (Software) wacce zaka iya amfani da ita wajen neman ta fassara maka wani harafi, kalma, jimla cikakkyiya da dai sauran makamantansu, daga wani harshe zuwa wani harshe, sabanin Dictionary wanda shi ya ta'allaka ne wajen fayyace maka bayanin da ya shafi Kalmomi,

    Kamar yadda na fada cewa wannan manhaja tana fassara wani harshe zuwa wani harshe, to haka abun yake, 

   misali:- Daga yaren Turanci zuwa Hausa, Hausa zuwa Turanci, Larabci zuwa Turanci, Turanci zuwa Larabci, da dai sauran su, domin kuwa akwai harsuna da dama a cikin wannan manhaja.

    Kasan cewa ta Dan karami a cikin daliban Illimi yasanya naga dacewar na bada gudunmawa ta zuwa ga Yan uwa Dalibai iri na, wanda bamu iya magana da yaren turanci ko larabci ba, a wasu lokutan har yaren mu na Hausar, yakan Wahalar damu,

  <•> Kwarewar ka wajen iya turanci bashi yake nuna Cewar bazaka yi amfani da wannan software ba.


YADDA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN Manhaja (SOFTWARE)


   Da farko dai zaka ziyar ci rumbun Adana Manhajoji (Playstore), sai ka rubuta GOOGLE ONLINE TRANSLATOR, daganan zai nuna maka manhajar, sai ka sauke ta akan wayarka ta hannu (Installed), daga nan kuma sai ka fara amfani da manhajar ta hanyar rubuta mata abun da kake bukatar ta fassara maka, tareda baka ma'anar da ta dace da abun da ka rubuta Mata. 


Rubutawa🖊️ Khalil Shuaibu Garunbabba ASOF member. WhatsApp/Call 07048767377.
Post a Comment (0)