HUKUNCIN DAKATAR DA JININ HAILA DOMIN TA AZUMCI RAMADAN


https://chat.whatsapp.com/D3VpiJzm6WECmizK6DEBfi
*_HUKUNCIN DAKATAR DA JININ AL'ADA DOMIN MACE TA AZUMCI RAMADANA GABA DAYA_* 



*TAMBAYA*❓

Aslm mala antashi lfy Allah yakara hasken ilimi ga tambayata wai ya halasta mace tasha maganin da zai tsayarmata da jinin al.ada don karta sha azumi


 *AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Mallaman wannan zamani, sun bayar da fatawar halascin yin haka, wato mace ta sha maganin da zai tsaida mata al'adar ta, don ta azumci watan Ramadan gaba ɗayan sa, amma da sharaɗin hakan ba zai cutar da ita ba. Daga cikin waɗannan Mallamai akwai Shaikh Bn Baaz da Shaikh Muhammad Salih Uthaimin rahmatullahi alaihima. 

Wannan fatawa zaka same ta a littafin risalatu fiddima'i aɗɗabi'iyyati linnisa'i na Mallam Uthaimin.

Ga kuma fatawar Bn Baaz nan lokacin da yake bayar da amsa ga mai neman fatawar 

لا حرج في ذلك أن تأخذ الحبوب لمنع الحيض حتى تصلي مع الناس، وتصوم مع الناس، بشرط أن يكون ذلك سليماً لا يضرها، عن مشاورة للطبيب، وعن موافقة من زوجها، حتى لا تضر نفسها، وحتى لا تعصي زوجها، فإذا كان عن تشاور، وعن احتياط من جهة السلامة من الضرر، فلا بأس. وهكذا في أيام الحج. نعم.
المقدم: بارك الله فيكم.

Wallahu ta'aala a'lam.
Post a Comment (0)