HUKUNCIN TABA JIKIN MACCE WADDA BA MUHARRAMABA?



اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

✍🏻Daga Zauren
     📌 *Albahral Ilmu*🌴

HUKUNCIN TABA JIKIN MACCE WADDA BA MUHARRAMABA?

 *TAMBAYA* ❓

Assalamualaikum Warahmatullah 🙋‍♂️
Malam Barkha Da Asbha Daphatan Kha Tashi Lapia

*Malam Dan Allah Meye Hukunchin Namijin Da Yah Ta6a Matar Aure? Ammah Kumah Shii Saurayine Bha Me Aure Bha?*


*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Lallai Allah madaukakin sarki idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da zata kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu ne tattaba ko shafar jikin mace babbar hanya ce wadda ke motsarda sha’awa zuwa ga aikata zina, kuma mun sani zina tana cikin zunubai guda bakwai wadanda suke da saurin hallakar da mutum. Bayan yin shirka da Allah sai kuma zina, saboda muninta Allah yace kada ma mu kusanceta. 

Hadisi ya tabbata wanda manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) yace:

*( Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe akan dayanku shi yafi masa alkhairi akan ya shafi jikin macen da bata halalta agareshi ba )*. Albany yace hadisine ingantacce acikin sahihul jami’ul kabeer (5045).

Haka kuma babu makawa yayin wannan shafe-shafen dole ayi zinar ido, zinar kunne, zinar harshe da kuma zinar kafa. Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Hurayrah (Allah ya yarda dashi) Annabi (sallallahu Alaihi wasallam) yace: *”Allah yana rubutawa dan Adam kasonsa na zina, zai riski wannan kason babu makawa, zinar ido itace kallo, zinar kunne saurara, zinar harshe zance, zinar kafa tafiya, zuciya tai buri tai sha’awa, farji shi zai yarda ko ya karyata”* Saboda haka ka sani zina kake aikatawa, amma duk da yake wannan bai kai zina ta asali girman laifi ba kuma babu wani haddi da shari’a ta hukuntar aiwa mutum anan duniya akansa akwai muni sosai a cikinsa.

kuji tsoron Allah ku tuba tun kafin lokaci ya kure muku, ku lazumci yiwa Allah biyayya cikin abunda ya haramta na dokokinsa, na daga abunda shafar mace yake haifarwa wanda yake kaiwa zuwa ga fitintunu da alfasha kala-kala. 

WALLAHU A'ALAM

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
0706746551
  
جزاكم الله خيرا و احسن الجزء
Post a Comment (0)