Labarin Farfesa da mai fito a kogi
*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*
Wata rana wani babban farfesa na ilimin kimiyya ya tashi zuwa wani gari. A cikin halin tafiya sai ya kawo bakin wani kogi inda ake fito da É—an wani jirgi. Duk wanda zai tsallake kogi yakan biya kuÉ—i kafin ya shiga jirgin. Farfesa ya ba da nasa kuÉ—in ya ce a ba shi shaida, wato rasit. Mai jirgi ya ce shi ba ya ba da wata shaida. Shaidarsa kawai shiga jirgi a haye da mutum. Sai Farfesa ya matsa da cewa a ba shi a rubuce. Mai jirgi ya ce, "Ai ni, ban iya rubutu ba."
Farfesa ya ce, "Tun da ba ka iya rubutu ba ka yi zaman duniya a banza." Mai jirgi dai ya yi gunaguni, a kan oho, a je ya yi zaman duniya a banza ɗin. Duk fasinjoji suka shiga tare da Farfesa, mai jirgi ya tuƙa
An yi nisa an rage gaci kaɗan sai kuwa sabon rusan ya kawo yana tambal-tambal da jirgi. Sai mai jirgi ya ce," Ya ku jama'a da ya juye na ga ya fi kyau kowa ya yi tsalle ya faɗa ya yi iyo ya ƙarasa gaci.".. Kafin a ce me kowa ya yi tsalle ya yi iyo ya kai gaci. Farfesa yana zaune. Mai jirgi ya ce, "To Farfesa sai ka faɗa domin ni ma zan tafi in bar jitgin.".. Sai ya ce, "Ai ban iya ruwa ba." Mai jirgi ya ce, "Ba ja iya ruwa ba? In haka ne ka yi zaman duniya a banza." "Ya daska tsalle ya haye ya bar Farfesa."
Shi wani darasi ku ka koya a cikin wannan labarin?
Daga: Littafin Hikayoyin Kaifafa Zukata, Littafi na É—aya (1), wallafar Malam Aminu Kano Rahimahullah.
*12th Rajab, 1442A.H (24/02/2021).*