HUKUNCIN TARA FARCE


*HUKUNCIN TARA FARCE💅🏻* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

SHIN KOYA HALATTA BARIN AKAIFA ( FARCE)?
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .
*AMSA*👇

 Yanke farce yana cikin sunnoni na dabi'a da'aka dabi'antar da mutum akansu saboda fadin
Annabi Sallallahu Alaihu wasallam ( Abubuwa biyar
suna daka dabi'ar da'aka halicci mutum dasu, kaciya, da aske gashin gaba, da rage gashin baki ga ( maza) da yanke farata, da tsige gashin
hammata) Bukhari da Muslim.
Yatabbata awasu hadisai sunnonin fidra guda gomane daka ciki akwai yanke farce, yazo ahadisin Anas dan malik Allah yakara yarda dashi yace:
( Annabi Sallallahu Alaihu wàsallam ya iyakance mana lokacin yanke gashin baki dayanke farce da
aske gashin gaba da tsige gashin hammata kada mubarshi yahaura kwana arba'in bamu kawar dasu
ba).
Ahmd, Bukhari, Nisa'i
Wanda bai yanke farcensa ba yasabawa sunnah, hikimar hakan shine tsafta da kuma fitar da abundake karkashinsu na dauda da datti, da dauke
kamanceceniya dawanda basa hakan cikin kafirai, dakuma kama da dabbobi,
Fatawa lajnatul da'imah ( 5/173).

Mafiya yawan mata ayau sun fada cikin
kamanceceniya da dabobi da dakafirai wajan tara farce, sannan sai su rinashi💅🏻 dajan farce baiki ko jah, wannan yakai makura wajan muni, da abun kyama acikin zukata, ga duk wani mai hankali mai
dabi'a kubutacciya.
Haka yana daka cikin mummunar dabi'a wajan wasu mutane saisu bar wani sashi nafarcen yai tsawo bakyan gani, dukkan wadannan sun sabawa sunnah da kuma fidira ta dan adam, saboda haka
bashi halatta tara farce gaba dayansa ko barin wani daka cikin faratan domin kamace dakafirai kama dakafirai kuma haramunne acikin dukkan komai na al'adunsu, Muna rokon Allah kubuta daka
wadannan munanan halaye, Allah yashiryar damu hanya madai-daiciya.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻠﻢ ﻟﻨﺎ ﺇﻻ ﻣﺎ ﻋﻠﻤﺘﻨﺎ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ
ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ .

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)