HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE




اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Daga Zauren 
📌 *Albahral Ilmu*🌴

✍🏻Rubutawa
      Abdulkadeer Umar Alshinkafawy.

*HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE* 


 *TAMBAYA* ❓

Assalamu alaikum malam, tambaya ce dani. Mijina ne yasake ni sau biyu, sai yasha abin maye yace na zo nasameshi, ni kuma banzoba saboda bana son abin da yakesha na maye, shine yace idan banzoba a bakin aure na. Shin yaya auren mu? Allah ya saka da alheri.


 *AMSA* 👇

Wa'alaikum assalam

 Malamai sun yi sabani game da aukuwar sakin wanda yake cikin maye:

1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan ya saki matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon Allah ne, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za'a yi masa uzuri ba, wannan ita ce maganar Abu-hanifa da Malik da Shafii a daya daga cikin zantukansa.

2. Sakinsa bai auku ba, saboda lokacin da Ma'iz ya zo ya tabbatarwa Annabi ﷺ ya yi zina saida ya tambaye shi ko ka sha giya ne, kamar yadda Baihaki ya rawaito a Sunanul-kubrah, hakan sai ya nuna mashayin giya ba'a amsar maganarsa.
Sannan an rawaito daga sayyadina Usman da Ibnu Abbas cewa: sakin mashayin giya ba ya aukuwa, kuma ba'a san wanda ya Saba musu ba a cikin Sahabbai.
Wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.
Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da yake fada ba, hakan sai ya sa ya yi kama da Mahaukaci wanda Alkalami ya saraya daga kan shi, kai har sallah ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'i ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
Don neman karin bayani duba: Al-Mugni 7/289 da kuma Sharhul Munti'i 10/233.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Post a Comment (0)