Shrin: *MATA TUBALIN AL’UMMA*
Rubutawa: *ZAINUDDEEN ZAIN* _DR.ZAIN_
Maudu’i: _wa cece kishiya? Ya ya dace a zauna da kishiya?_
*KISHIYA* : kalma ce da ke nuna haduwar abubuwa guda biyu karkashin abu daya, ta inda ko wanne daga cikin nau’I na abu biyun, ke kokaarin zama gwani ko tozali a idanun abinda suke kishi a kai. A auratayya, kishiya wata halattaciyar mace ce da ubaangiji ya yi umarni da mazaje su mallaka, ma’ana su auri mace biyu har zuwa uku, matsawar suna da yakinin yin adalci a tsakanin matan.
Kishiya zamu iya kirantaa wata abokiyar zama da ake aurowa mace a gidan mijinta, wacce za ta zama abokiyar rayuwarta da shi mijin nasu har ya zuwa karshen rayukaansu.
Ubangiji shi ya yi umarni ga mazaje da su auri mace sama da daya *(Qur’ani Surah ta 4 aya ta 3).* Idan haka ne kuwa saninmu ne ubangiji da ya halicci dan”adam ya fi sonsa fiye da mahaifiyarsa, akwai hadisin manzo Allah SAW da yazo, bayan kammala yaki, sai suka ga wata mata tana tona gawarwakin mutane tana kuka, sai cen ta ga dan karamin danta, ta dauko shi ta rungume kamar ta hadiye shi, sai manzon Allah ya ce; “kuna ganin waccen matar za tai ya kada danta cikin wuta?” sahabbai suka amsa da “ko da alama ya manzon Allah” sai ya ce; “ubangiji da ya halicce ku, ya fi ku tausayin kawunanku, fiye da tausayin matarnan zuwa ga danta”. Na kawo wannan domin na nuna muna cewa, ubangiji ba ya umarni da abinda zai cutar da mu, da ace kishi mugun abu ne da ubangiji bai ba wa maza dmar karo aure ba.
Ga wata tambaya da members na *MATA TUBALIN AL’UMMA* suka min “_Dr. Zain; da ace matarka za ta karo aure, ko ka tabbatar budurwarka tana tare da wani ya za ka yi/ji?”_ sai a lokacin na kara fahimtar dalilai da ya sa ubangiji bai shari’anta maza su yi kishi ba ta hanyar auren maza sama da daya, domin shakka babu, za a yi kashe-kashe. Su kuwa mata ubangiji ya halicce su da sanyin zuciya da iya barin abu a rai komai zafinsa, da kuma rauni musamman na girman kwakwalwa (inji malaman kimiyya) kan wannan sai ya halatta su yi kishi, saboda za su iya dauka.
*YADDA YA KAMATA A ZAUNA DA KISHIYA*
Tunda addini bai haramta zama da kishiya ba, ba shakka dole addini ya shimfida yadda ya kamata zaman kishiyoyi ya kasance, a rubuce ko a tarihance. Bamuda babban misali na zaman kiyoshi fiye da zaman matan manzon Allah SAW ga wasu daga halayyar da ya dace kiyoshi su dinga kasancewa a kai:
*TAKARA WURIN FARANTAWA MIJI RAI*: maza da dama ana burge su ne idan ana faranta musu rayuwa, duk da sakin fuska da adalci irin na manzon Allah, idan ya shiga dakin Zainab yakan dade, har matansa suka fara tsarguwa a haka, sai daga baya suka fahimci ashe zuma take bashi, shi kuwa Allah ya halicce shi da son zuma, ‘yaruwa, me zai hana ki fahimci abinda mijinki ya fi so kema ki dinga birge shi da shi, domin ki sami kujerar zama a gidanki? Ki lura idan ya fi son kwalliya ta guntun skirt ko jeans da dai sauransu, sai ki dinga yi masa, ki gani yadda hankalinsa zai dawo kanki. Haka ake kishi, ba kullum saai makota sun shigo rabon fada ba.
*TAKARA WURIN TAIMAAKA MASA*: wasu mata, ko sunada abin hannunsu, sun fi so namiji ya ba da nashi a kashe, wannan halayyar ko ba kya da kishiya bai dace ba, amfi so ki dinga tausayawa mijinki kina taimaka masa musamman a cefane da sauransu, ba kullum bani-bani ba. A lokacin da kike yawan rokonsa, ita kuma kishiyarki tama tausaya masa kuma tana taimakonsa, sai kigaa ta kwace gida, ki dawo aza annu a ka kina fadin “ta sihirce shi” bayan laifinki ne. rayuwa fa tanason mai tausaya masa.
*TAKARA WURIN TSAFTA*: tsafta abar so ce kusan a kowacce al’ada haka a dabi’ar dan’adam, idan kishiyarki ta fi ki iya tsafta, gaskiya kina cikin damuwa.
Wadannan kadan kenan kan yadda ya kamata mata su yi kishi a gidajensu ba wai fadace-fadace ba.
Haka yanada kyau, abokan zama (kiyoshi) su hada kawunansu a gidajen mazajensu, susan cewa a gobe kiyama, za’a tambaye su kan irin zama da suka yi da junasu, kar ki kalli kishiya a matsayin makiyiya ko wata muguwa, ki mu’amalance ta a matsayin kanwa ko yaya, haka sai kiga shi karan kansa mijin naku sai ya rasa wace yafi so, kuma duk yadda yaso ya nuna bambanci idan kawunanku suna hade, ba yadda ya iya, dole ya kwatanta.
*KIRA GA MAZA*
Inaso nayi amfani da wannan gabar na kira hankulan maza musamman masu nuna bambanci tsakanin matansu a bayyane, ubangiji ya fada duk yadda muka so ba zamu iya yin adalci dari bisa dari ba, haka zancen yake, amma ko da a ranka ka fi son daya, sai ka bar wannan sirrin a zuciyarka, ka yi mu’amala da kowacce yadda addini ya umarce ka. Mu sani fa, duk wanda baiyi adalci ba a tsakanin matansa, ubangiji zai tada shi rabin jikinsa a shanye.
Wasu maza idan suka lura kawunan matansu na a hade, su kuma gasu da son tada fitini, sai su koma annamimai, su dinga shiga da fita ta yadda zasu raba kawunan matan ta hanyar guntayen maganganu, wannan ma babban laifi ne a wurin ubangiji.
Allah yaimunaa jagora.
*DR. ZAIN*
*MATA TUBALIN AL’UMMA*