*NADAMAR BAYAN MUTUWA*
-
GABATARWA:
Muhammad Umar Baballe.
-
"Haƙiƙa sau da yawa a wannan duniyar akanyi nadama bayan aikata kuskure sannan kuma nadamar tayi amfani, amma a ranar lahira nadama bata sanya mai yinta ya samu sauƙi daga cikin takaicin da yake addabarsa a gaban Allah"
-
"Anan duniya zaka iya aikata wani abu mara kyau, sannan daga baya kayi nadama ta zamto maka alkhairi kuma tasa ka sami yarda daga gurin mutane, amma a ranar lahira nadama abinda ke bin bayanta shine asara"
-
"Daga lokacin da aka binne ɗan adam, shikenan ya shiga cikin kogin yin nadamar me yasa bai aikata abu kaza da kaza ba, me yasa bai yiwa Allah biyayya a lokaci kaza ba, me yasa bai tsaya ya bautawa Allah yadda ya dace ba"
-
"Wannan nadama ce wacce bata da amfani, domin lallai amfaninta a duniya yake, to shi kuma ya riga ya bar duniyar, kaga kenan babu damar yin gyara balle nadamarsa tayi masa amfani"
-
"Wallahi bayan mutuwar mutum, zai so ace Allah ya ara masa koda second guda ne domin ya dawo wannan duniyar yayi wa Allah sallah koda raka'a ɗaya ce, to amma babu wannan damar, damar sa ɗaya ce, itace lokacin da yake a raye, to shi kuma yayi wasa da ita yau gashi har ya bar duniyar"
-
"Mutane sukan aikata zunubai masu tarin yawa, suna zullumin cewa ai nan gaba zasu tuba, sun manta da cewa ikon karɓar rayuwarsa ba a hannayen su yake ba, Allah ne kaɗai yake da sanin ranar mutuwar kowa"
-
"Sai bayan sun gama tafka kuskurensu, a ranar lahira kuma suzo da fuskar tausayi suna nuna nadama, alhalin kuwa wannan baza tayi musu aiki ba"
-
Ya Allah ka raba mu da yin nadama a ranar lahira, Ameen.
-
✍🏿Muhammad Umar Baballe