SHAWARA AKAN NEMAN AURE WACCE AKAYI LALATA DA ITA
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
*TAMBAYA*❓
Aslm amincin Allah a gareka ya malam y kk y gd kuma to Allah yasa aljannane mako marka Ameen ya Allah .malam don Allah ina neman shawaranka ne kuma da yaya matsayin abun a musulunci malam nine nakasance nafara son wata yarinyar tun da yarinta kuma ga shi mun girma a she ita tana nan tana sona nima kuma har ga Allah ina sonta malam saide matsala guda daya malam nayi buncike a kanta malam gaskiya nasamu labarin wai antaɓa yi lalata da ita anma kuma ita taki tafadamun to shine na kuma ita tana sona malam to shine nake nemar shawaranka xan iya sonta ko kuma naya hakuri don har ga Allah ina son nayi aure ne shiyasa nake neman shawaranka malam Allah yayi albarka Ameen Nagode.
*AMSA*👇
Idan ka san wannan Ba zai zama matsala a gareka ba, zaka Iya Aurenta.
Idan Kuma kasan wannan zai Iya sanadin Ka Wulakanta ta ko ka Goranta Mata ko ka cutar da ita ko ka tsane ta daga baya. To Maganar gaskiya Kar ka sake ka Karbi Soyayyar ta. Ka yi Mata Addu'ar Allah ya kawo Mata Na Gari. Kuma Kar ka Gayawa kowa halin da ta taba Tsintar kanta a Ciki.
Akwai Mutumin da Zai Auri Mace kuma Yimata Gorin Wani Abu da ya Faru da ita a Rayuwa. To idan Kasan ba zaka Iya Hadiye Wannan Aibun da yake Tare da ita ba, to Kar ma ka Fara Neman Auren ta.
Sannan Kuma Wajibi ne ka Rufa Mata Asiri. Kar ya Gayawa kowa. Sabida idan ka Ci gaba da Gayawa Mutane. Ba zata Sami Mijin Aure ba. Ka ga Kuma wannan Ba Daidai bane. Domin ba Wanda zai Auri Macen da yasan Wani Namiji yayi Lalata da Ita.
Allah ya Kare mu ya kare mana Zuri'armu.
Allah Shine Masani.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*