*ALAMUN ƊAN ALJANNAH:*
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
*TAMBAYA*❓
_As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah_ .
Wai waɗanne alamu ne suke tabbatar wa mutum cewa Aljannah ce makomarsa a bayan mutuwa?
*AMSA*👇
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .
[1] Abin da muka sani dai shi ne siffofin ’yan Aljannah a dunƙule kawai. Allaah Ta’aala ya ce:
۞ وَسَارِعُوۤا۟ إِلَىٰ مَغۡفِرَةࣲ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَـٰوَ ٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِینَ
ٱلَّذِینَ یُنفِقُونَ فِی ٱلسَّرَّاۤءِ وَٱلضَّرَّاۤءِ وَٱلۡكَـٰظِمِینَ ٱلۡغَیۡظَ وَٱلۡعَافِینَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ یُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِینَ
وَٱلَّذِینَ إِذَا فَعَلُوا۟ فَـٰحِشَةً أَوۡ ظَلَمُوۤا۟ أَنفُسَهُمۡ ذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ فَٱسۡتَغۡفَرُوا۟ لِذُنُوبِهِمۡ وَمَن یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَلَمۡ یُصِرُّوا۟ عَلَىٰ مَا فَعَلُوا۟ وَهُمۡ یَعۡلَمُونَ
أُو۟لَـٰۤىِٕكَ جَزَاۤؤُهُم مَّغۡفِرَةࣱ مِّن رَّبِّهِمۡ وَجَنَّـٰتࣱ تَجۡرِی مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَـٰرُ خَـٰلِدِینَ فِیهَاۚ وَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَـٰمِلِینَ
*Kuma ku yi gaggawa zuwa ga samun gafara daga Ubangijinku da samun Aljannah faɗinta kamar faɗin sammai da ƙasa, an yi tattalinta domin masu taqawa. Waɗanda suke ciyarwa a cikin wadata da ƙuncin rayuwa, kuma masu kame fushi, masu yafewa ga mutane, kuma Allaah yana son masu kyautatawa. Kuma waɗanda idan suka aikata alfasha ko suka cuci rayukansu sai su tuna Allaah sai kuma su nemi gafara domin zunubansu, kuma wanene yake gafarar zunubai in ba Allaah ba, kuma ba su dogewa a kan abin da suka aikata alhali kuwa suna sane. Waɗannan sakamakonsu gafara ce daga Ubangijinsu da wata Aljannah wacce ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinta, suna madawwama a cikinta, kuma madalla da ladan masu aiki.* _(Surah Al-Imraan: 133-136)._
Sannan kuma ya ce:
۞ أَفَمَن یَعۡلَمُ أَنَّمَاۤ أُنزِلَ إِلَیۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰۤۚ إِنَّمَا یَتَذَكَّرُ أُو۟لُوا۟ ٱلۡأَلۡبَـٰبِ
ٱلَّذِینَ یُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا یَنقُضُونَ ٱلۡمِیثَـٰقَ
وَٱلَّذِینَ یَصِلُونَ مَاۤ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦۤ أَن یُوصَلَ وَیَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَیَخَافُونَ سُوۤءَ ٱلۡحِسَابِ
وَٱلَّذِینَ صَبَرُوا۟ ٱبۡتِغَاۤءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُوا۟ مِمَّا رَزَقۡنَـٰهُمۡ سِرࣰّا وَعَلَانِیَةࣰ وَیَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّیِّئَةَ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
جَنَّـٰتُ عَدۡنࣲ یَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَاۤىِٕهِمۡ وَأَزۡوَ ٰجِهِمۡ وَذُرِّیَّـٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَـٰۤىِٕكَةُ یَدۡخُلُونَ عَلَیۡهِم مِّن كُلِّ بَابࣲ
سَلَـٰمٌ عَلَیۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
*Shin wai wanda ya san cewa: Duk abin da aka saukar maka da wurin Ubangijinka shi ne gaskiya yana yin daidai da makaho? Masu hankali ne kaɗai suke yin tunani. Waɗanda suke cika alƙawarin Allaah kuma ba su warware alƙawari. Kuma waɗanda suke sadar da abin da Allaah ya yi umurnin a sadar da shi, suke tsoron Ubangijinsu, kuma suke tsoron mummunar hisabi. Kuma waɗanda suke yin haƙuri don neman Fuskar Ubangijinsu, suke tsai da Sallah kuma suke ciyarwa daga abin da muka azurta su da shi, ko a ɓoye ko a bayyane, kuma suke tunkuɗe mummunan aiki da kyakkyawa. Waɗannan su ke da ƙarshen gida mai kyau. Aljannar Dawwama ce za su shige ta tare da duk wanda ya kyautata daga cikin iyayensu da matan aurensu da zuriyarsu, kuma mala’iku suna shiga gare su ta kowace ƙofa. Suna cewa: Amincin Allaah ya tabbata a gare ku. Madalla da ƙarshen gida mai kyau!* _(Surah Ar-Ra’ad: 19-24)_
Haka wannan bayanin ya zo a cikin Ayoyi da yawa na Alqur’ani, kamar: Surah Al-Mu’minuun: 1-11; Surah Al-Furqaan: 63-76; Surah At-Taubah: 111-112; Surah Qaaf: 31-34; Surah Al-Ma’aarij: 22-35.
Duk wanda ya tsare irin waɗannan ayyukan a cikin Imani da Tsoron Allaah da koyi da koyarwar Sunnar Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ don neman kyakkyawan sakamako da tsoron azabar Ubangiji Ta’aal shi ne ake wa albishir da Gidan Aljannah a Lahira.
[2] Amma tabbatar da samun Gidan Aljannah ko Gidan Wuta ga wani mutum guda daga cikin musulmi masu fuskantar Alqibla a cikin wannan rayuwar ta duniya ba abu ne mai sauƙi ba, kuma ma ba mai yiwuwa ba ne. Sai dai ga wanda nassi sahihi kuma sarihi ya tabbata a kansa daga Allaah ko Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)._ Domin makomar mutane na Wuta ko Aljannah yana wurin Allaah ne, ka
وَلِلَّهِ مَا فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَمَا فِی ٱلۡأَرۡضِۚ یَغۡفِرُ لِمَن یَشَاۤءُ وَیُعَذِّبُ مَن یَشَاۤءُۚ وَٱللَّهُ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ
Kuma duk abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allaah ne kaɗai, Yana yin gafara ga wanda ya ga dama, kuma yana azabtar da wanda ya gadama, kuma Allaah mai yawan Gafara ne, mai yawan Rahama. _(Surah Al-Imraan: 129)._
Sannan kuma a ranar da Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya je dubo Sahabinsa Ka’ab Bn Ujirah _(Radiyal Laahu Anhu),_ da ya shiga wurinsa kuma ya ce: Ka’ab, albishirinka! Sai kuwa mahaifiyarsa ta ce: Kai Ka’ab! Ina maka murna da samun Aljannah! Sai Annabi _(Sallal Laa Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce: Wacece wannan mai yanke hukunci da rantsuwa a kan Allaah?! Ka’ab ya ce: Mahaifiyata ce! Sai Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:
وَمَا يُدْرِيكِ يَا أمَّ كَعْبٍ ؟ ! لَعَلَّ كَعْباً قَالَ مَا لَا يَعْنِيهِ ، أَوْ مَنَعَ مَا لَا يُغْنِيهِ
Me ya sanar da ke ne, Ummu-Ka’ab?! Wataƙila fa Ka’ab ya faɗi wani abin da bai shafe shi ba, ko kuma ya ƙi bayar da abin da ba zai wadata shi ba! _(Silsilah Saheehah: 3103)_
Don haka, mutum ya ayyana wa kansa ko waninsa cewa shi ɗin nan ɗan Aljannah ne ko ɗan Wuta, kamar shiga gonar Allaah Ta’aala ne kawai. Shiyasa dole a nan sai kowa ya tsaya ga irin abin da Allaah ko Manzonsa _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ suka faɗa kawai.
(i) Allaah ya tabbatar da shiga Wuta ga Fir’auna da Abu-Lahab da makamantansu daga cikin la’antattu.
(ii) Kuma Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya tabbatar da samun Aljannah ga Manyan Sahabbansa guda goma (Abu-Bakar As-Siddeeq, Umar Bn Al-Khattaab, Uthmaan Bn Affaan, Aliy Bn Abi-Taalib, Sa’ad Bn Abi-Waqqaas, Sa’eed Bn Zaid, Abdurrahman Bn Auf, Dalhah Bn Ubaidillaah da Zubair Bn Al-Awwaam), da Fatimah Bint Rasuulil Laah, da Al-Hasan, da Al-Husain Ibnai Aliy Bn Abi-Taalib, da Bilaal Al-Mu’azzin, da Abdullaah Bn Salaam, da Ukkaashah Bn Mihsaan, da baƙar matar nan wacce ta zaɓi yin haƙuri da matsalar farfaɗiya a kan samun waraka daga addu’arsa _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ da sauransu dai masu yawa _(Radiyal Laahu Anhum)._ Waɗannan duk muna tabbatar musu da samun Aljannah kamar yadda Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya faɗa.
(iii) Waɗansu malamai kuma sun ƙara a cikin masu samun Aljannah akwai duk wanda jama’ar musulmi na kirki suka haɗu a kan yi masa kyakkyawar yabo na kirki a bayan mutuwarsa. Sai dai kuma wannan maganar ba ta kai ta sama ƙarfi ba, domin samun haɗuwar mutanen kirki a zamunnan nan na ƙarshe abu ne mawuyaci. Sannan kuma ga yadda mutane suke amincewa da yarda wasu ayyukan mutum na rayuwar duniya kawai ba addini ba!
Wannan matsayar ta rashin yin shisshigi a kan ambata wa wani cewa shi ɗan Aljannah ne ko ɗan Wuta ita ce *Aqidar Ahlus-Sunnah* , saɓanin ’yan bidi’a daga cikin *Mu’utazilah* da *Khawaarij* da *Raafidah* da sauransu waɗanda suke shigar da wanda suka ga dama a cikin Aljannah, kuma suke shigar da wanda suka ga dama a cikin Wuta.
Al-Imaam At-Tahaawiy ya faɗa a cikin Littafin Aqidarsa (#70) cewa:
وَلَا نُنْزِلُ أَحَدًا مِنْهُمْ جَنَّةً وَلَا نَارًا ، وَلَا نَشْهَدُ عَلَيْهِمْ بِكُفْرٍ وَلَا شْرِكٍ وَلَا نِفَاقٍ ، مَا لَمْ يَظْهَرْ مِنْهُمْ شَيْءٌ مِنْ ذَلِكَ ، وَنَذَرَ سَرَائِرَهُمْ إِلَى اللهِ تَعَالَى
Kuma ba mu shigar da wani ɗaya daga cikin masu duban Alqibla a cikin Aljannah ko Wuta, kuma ba mu yin shaida a kansu da kafirci ko shirka ko munafunci, matuƙar dai wani abu na hakan bai bayyana daga gare su ba, kuma muna ƙyale sirrinsu ga Allaah Ta’aala kawai.
Allaah ya shiryar da mu.
_Wal Laahu A’lam._
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*
