SHI SOJA NE… BA YA RABON KWANA


SHI SOJA NE… BA YA RABON KWANA

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

_As-Salamu Alaikum,_
Mijina soja ne, kuma tun aurenmu ba mu taɓa zama tare na watanni biyu ba. Amma idan ya yi sabon aure sai ya zauna da amaryar a inda ya ke, kuma ko da watanni nawa zai yi, ba tare da izinina ko neman yardata ba. Idan na yi magana sai ya ce wai ni saboda yara ba zai yiwu in bi shi ba! Sai dai yana turo mini kuɗin abinci da na makarantar yara a kan lokaci, kuma bayan watanni 3 - 4 yakan zo in ya samu pass. Matsalata ita ce, tun da bai nemi izinina ba, to yanzu idan na bar su da Allaah, na yi Allaah-ya-isa Allaah zai saka min?


*AMSA*👇

_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._
Yin ƙarin aure a musulunci yana tattare ko nannaɗe ne da sharaɗin iya yin adalci cikin abubuwan da suke a fili a bayyane a tsakanin matan. Duk lokacin da namiji ya ji tsoron cewa ba zai iya yin irin wannan adalcin a tsakanin matansa ba, to bai halatta ya ƙara aure ba. Tun da duk wanda yake haka an yi masa alƙawarin samun matsanancin azama mai raɗaɗi a Lahira. Maimakon haka sai ya je ya auro kuyanga ko sa-ɗaka, a lokacin da ake da su.
Daga cikin irin waɗannan abubuwan da ya zama wajibi tilas miji ya yi adalci a tsakanin matansa a ciki, akwai rabon-kwana a tsakaninsu. Ba bambanci ko a gari ɗaya suke ko a mabambantan garuruwa ne, duk ɗaya ne. Idan ba zai iya haɗa su a wuri guda ba, to sai ya riƙa kiran wacce take nesa, ko ya ɗauko ta ya kawo ta inda ya ke a lokacin rabonta, ko kuma shi ya riƙa tafiya yana samunta a inda ta ke.
Rashin lafiya, jego, jimamin mutuwa ko asara, sana’a ko aikin ofis, samun baƙin girma na mutunci, yawan ’ya’ya da makamantan haka duk ba uzurori ne da suke kayar da haƙƙin mace, su hana a yi rabon kwana na adalci a tsakaninta da sauran kishiyoyinta ba, a mahanga ta shari’a.
Wajibin da ke kan duk waɗanda suka samu irin wannan matsalar shi ne: Su zauna su yi yarjejeniya da matar tukuna tun da farko. Sai in ta amince, ta yarda da ajiye haƙƙin kwananta, ko ta bayar da kyautansa ga mijin ko ga wata daga cikin kishiyoyinta, ko kuma ita ce da kanta ta ƙi yarda ta tafi inda mijin ya ke, to a sannan ne kawai za a iya ƙyale ta a wani gari, a tafi da amarya zuwa wani garin na daban.
Da zaran an samu irin wannan amincewa da yarjejeniya, shikenan sai su cigaba a kan haka. Idan kuma daga baya suka ga dacewar su sake zama domin sake yi wa yarjejeniyar kwaskwarima ko gyarar fuska duk daidai ne. Haka kuma ko idan daga baya ita matar ce ta ga shirin bai yi mata ba, ya gano cewa ƙwara ko cuta ya bayyana a cikin wannan tsarin, to tana iya neman a sake zama domin a gyara shi. Tana da dama, in ji malamai, ta dawo ta ce kyautar da ta bayar na kwananta ga mijinta ko ga kishiyarta ta fasa. Yanzu a ba ta haƙƙinta.
Bin wannan matakin shi ya fi alkhairi fiye da abin da kike tunani ko ƙoƙarin yi na yi musu Allaah-ya-isa, wai don kawai ba a nemi yardarki ba. Don haka kuma har ba ki bari a yi zaman lafiya da kishiyar!
Sannan ko da mijin ya cije a kan ƙin bayar da wannan haƙƙin ga matarsa, shawarar da muke bayarwa ga mata a yau ita ce: Duk da haka bai halatta ita kuma ta tsaya yin faɗa, ko tayar da jijiyoyin wuya a kan ƙwato wannan abin da ƙarfi ba, musamman a gaban ’ya’yanta waɗanda take neman ɗora su a kan kyakkyawar tarbiyya. Maimakon haka, gara ta ɗauki maganar zuwa gaba, wurin manyan da suka ɗaura auren tun da fari, don neman mafita. Duk irin abin da suka yanke sai ta yi haƙurin ɗaukarsa haka, tare da yawaita addu’o’in neman alkhairi a nan duniya da makoma lahira.
A ƙarshe dole shi ma mijin ya san cewa: Matar da ya aura kuma ya ajiye ta a nan, ya san cewa fa ita ba bishiya ce ko bangon ɗaki ba ne. Lallai ya san cewa ita ma mutum ce mai jini da tsoka, kuma mai lafiyayyar zuciyar da take harba jini zuwa sassan jikinta. Don haka, ba daidai ba ne ya ɗauka wai tun da ta haihu shikenan yanzu sha’awarta ta kare, ta koma babu wani abu a gabanta sai tarbiyyar ’ya’ya kawai. Shi kuma abin da ke aikinsa a wurinta shi ne kawai ya cigaba da aiko mata da kuɗaɗen abinci da magani da na makarantar boko da Islamiyyah!
Shi ma da ya ke soja, wanda a kullum yake cikin hatsari ko barazanar samun naƙasa ko ma rasa ransa a filin daga, ko ta hannun ’yan ta’adda masu neman hallaka shi… shi bai manta da sha’awar saduwa ba, don haka ne ma yake ta ƙara aure..., sai matarsa ce wacce ba ta cikin irin waccan hatsarin ko barazanar za a ce sha’awar ba za ta dame ta ba?!
Dole maza su san cewa, su ma mata suna da tsananin sha’awar irin abin da maza suke sha’awa a wurin mata. Don haka lallai kowane magidanci ya yi tsayin-daka wurin biya wa matarsa haƙƙoƙinta ba tare da rage komai ba, tun kafin zuwan ranar lahira: Ranar da za a mayar da haƙƙoƙi ga masu su, har a kai ga tambayar mutum a kan iyalin gidansa.
Allaah ya taimake mu, ya datar da mu ga dukkan alkhairi.
_Wal Laahu A’lam._

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)