HUKUNCIN KOME BAYAN SAKI UKU A DUNKULE A KALMA DAYA

HUKUNCIN KOME BAYAN SAKI UKU A DUNKULE A KALMA DAYA

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Malam mutumne yasaki matarsa saki uku adunkule a kalma daya ko arubutu daya- shin yanada ikon dawowa da ita⁉


*AMSA*👇

An yiwa SHEIKH ABDUL-AZIZ BN BAAZ RHMHLH irin wannan tambayar sai ya amsa da fuskoki 2=
1- Jamhuran Malamai sun tafi akan cewa wanda yayiwa matarsa saki 3 adunkule alokaci guda sa saku dukka 3 bashi ba auranta sai tayi sahihin aure in mijin ya mutu ko yasaketa bayan ya kusanceta in yaso tsohon mijin yasake aurenta in yana bukata, sun kafa Hujja da Hadisin ABDLH IBN ABBAS R/A
[ ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ : ‏] ﻛﺎﻥَ ﺍﻟﻄَّﻼﻕُ ﻋﻠﻰ ﻋَﻬْﺪِ ﺭَﺳﻮﻝِ ﺍﻟﻠﻪِ ﷺ، ﻭَﺃَﺑِﻲ ﺑَﻜْﺮٍ، ﻭَﺳَﻨَﺘَﻴْﻦِ ﻣِﻦ ﺧِﻼﻓَﺔِ ﻋُﻤَﺮَ، ﻃَﻼﻕُ ﺍﻟﺜَّﻼﺙِ ﻭﺍﺣِﺪَﺓً، ﻓَﻘﺎﻝَ ﻋُﻤَﺮُ ﺑﻦُ ﺍﻟﺨَﻄّﺎﺏِ : ﺇﻥَّ ﺍﻟﻨّﺎﺱَ ﻗَﺪِ ﺍﺳْﺘَﻌْﺠَﻠُﻮﺍ ﻓﻲ ﺃَﻣْﺮٍ ﻗﺪْ ﻛﺎﻧَﺖْ ﻟﻬﻢْ ﻓﻴﻪ ﺃَﻧﺎﺓٌ، ﻓﻠﻮْ ﺃَﻣْﻀَﻴْﻨﺎﻩُ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻓﺄﻣْﻀﺎﻩُ ﻋﻠﻴﻬﻢ .
ﻣﺴﻠﻢ ‏( ٢٦١ ﻫـ ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ١٤٧٢ • ‏[ ﺻﺤﻴﺢ ] •

Wato= ya kasance a zamanin ANNABI SAW da ABUBAKAR da shekaru 2 azamanin UMAR R/A- saki uku adunkule- saki dayane, daga baya UMAR yamaida ukun adunkulen uku ne yayinda yaga ana wasa da saki, (MSLM, SAHIH ABU DWD)

Don haka sukace tunda karshen lamari UMAR ya maida saki 3 yasaku 3 kuma SAHABBAI R/A basuja dashiba to don haka ba dawowa,

2- Wasu Ma'abota ilimi kuma sunce= saki uku adunkule saki dayane, tunda haka yake a zamanin ANNABI SAW da ABUBAKAR R/A kamar yadda yazo a hadisinda muka kawo abaya,
Kuma sun kafa hujja da Hadisin IMAM AHMAD daga IBN ABBAS
[ ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ : ‏] ﺃﻥ ﺃﺑﺎ ﺭﻛﺎﻧﺔَ ﻃﻠَّﻖ ﺍﻣﺮﺃﺗَﻪ ﺛﻼﺛًﺎ ﻓﺮﺩَّﻫﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﻨﺒﻲُّ ﷺ ﻭﻗﺎﻝ : ﺇﻧﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺓٌ
ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ‏( ١٤١٩ ﻫـ ‏) ، ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ٤٢٠/ ٢١ • ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ
Wato= ABU RUKANAH yasaki UMMU RUKANAH saki 3 adunkule sai ANNABI SAW yace dayane.
Kuma suka kafa hujja da fadin ALLAH SW a (SRT BQR-229)
ﺍﻟﻄﻼﻕ ﻣﺮﺗﺎﻥ
Wato= saki marra biyune,
Wato daya bayan daya ba dunkalasu alokaci daya,
Cikin wadanda suka tafi akan hakan cikin SAHABBAI Akwai (IBN ABBAS, ALIY IBN TALIB, ABDURRAHMAN IBN AWF, ZUBAIR IBN AWWAM, IBN MAS'UD, cikin TABI'AI akwai MUHD IBN IS'HAQ da dandazon Maluma, a 'yan baya akwai IBN TAIMIYYAH da dalibinsa IBNUL QAYYIM,
Kuma inji BN BAAZ- Wannan shine fatawata saki 3 adunkule 1 ne don aiki da nassosi da kuma rahama ga Musulmai, dubi-
(ALFATAWA- KITABUD-DA'AWA na BN BAAZ)
◼IBN HAJR yace= gameda Hadisin ABU RUKANAH- nassine akan saki 3 adunkule saki 1 ne babu tawili, (FAT-HUL BAARY)
◼IBNUL QAYYIM yace= Wannan ANNABINE SAW da kansa da KHALIFANSA ABUBAKAR R/A da dukkan SAHABBAI tun daga zamaninsa zuwa zamanin ABUBAKAR zuwa shekaru 3 na zamanin UMAR suna kan saki 3 adunkule 1 ne, da mai irge zai irga SAHABBANDA ke ganin saki 3 adunkule dayane SAHABBAN sunfi dubu, (ZADUL MA'AD & IGATSATUL LAHFAN & KHASHIYAR BUKUGUL MARAM)
◼IBN ABBAS (TURJUMANUL QUR'AN) shima kansa afarkon lamari yana bada fatawar saki 3 adunkule saki ukune, daga baya yasauko daga wannan fatawar yajenyeta yadawo zuwaga Saki 3 adunkule saki dayane,

 *NACE* 
A zamaninnan yafi dacewa murinjayarda fahimta na biyu, na saki 3 adunkule saki 1 ne domin ya sami asali tun daga ANNABI SAW👍🏻 kuma shine sauki akan nafarkon- kuma ALLAH SW yace <<ALLAH yana sonku da saukine baya sonku da tsanani>> Kuma yace <<ALLAH yanason yasassauta muku domin an halicci mutumne mai rauni>> kuma munada yawan mata da karancin maza da yawan fitintinun fasikanci da zinace zinace, yadace ayi aiki da wannan fatawar na ANNABI SAW don toshe barna‼
➖Kuma ya dace muyi aiki da hukuncin UMAR IBN KHATDAB yayinda mukaga maslahar rabuwar, kamar mijin hana zaluntarta da duka ko yunwa ko shaye shaye ko rashin ibada- sai yayi mata saki 3 adunkule sai azartar masa ukun, tunda UMAR R/A ya zartarne don maslaha kuma yana daga cikin KHULAFA'UR RASHIDEEN da ANNABI SAW ya umurcemu mubisu, kuma ALLAH SW yace <<mazaje nada ikon mayarda matayensune in sunso maslahane>> ashe in babu maslaha bai halattaba koda sakin dayane ballantana 3 adunkule.
ALLAHU A'ALAM.

*Amsawa :Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu*

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)