SOFTWARE ENGINEER: GABATARWA



An fara wannan darasi (softtware engineering.) a matsayin digiri a imperial college dake kasar london (UK)
a shekarar 1987...

Software Injiniyarin (01)

•°•°•°•SOFTWARE ENGINEERING
(GABATARWA)

wannan darasi na software engineering yasamu daga wani babban taro da kungiyar gamayyar turai wato (NATO) ta gabatar a shekarar 1968 da kuma 1969 domin tattaunawa akan matsaloli/rikice-rikice kokuma lalacewa ta manhaja da ake fama da ita a wannan lokaci wato shi akewa lakabi da (software crises) yayin samar da babbar hadaddiyar manhaja ba a kare wanan zama ba sai da aka samar da masalaha kan magance matsalolin rikicin manhaja wannan masalahar da aka samu ita ta haifar da softtware engineering.

 An fara wannan darasi (softtware engineering.) a matsayin digiri a imperial college dake kasar london (UK)
a shekarar 1987 haka yaci gaba da karbuwa a sassan duniya saboda inganci, dakuma saukaka rayuwa ta fannin fasaha.

ya taimaka wajen yaduwar ilimi dakuma karfafa alaka tsakanin al umma ma banbanbata...


ME NE NE SOFTWRE ENGINEERING?
Software engineering kan ayyanu a matsayin wani iimi da ake akan shiryayyen tsari,na horarwa ta musamman nunawa, gwada inganci, kiyayeywa/kula wajen kirkira da aiki dakuma aiki na manjaha(software).

AMFANI/ALHAKI NA SOFTWARE ENGINEER:

1.Dole ne yakasan ce mai dogon nazari akan abinda masu amfani da manhaja(software) ke bukata tare da kyakkyawan Adana Bayanai

2.yakasance mai binkice wajen tsarawa dakuma rubuta manhaja; misali kamar manhajar kasuwanci, manhajar koyo/koyarwa da ilimi, OS na na 'ura gabadaya DSS.

3.yakasance mai kimantawa(sanin amfaninta/illarta Ga al'umma) wajen kirkira manhaja takuma dace da yanayin tafiyar hardware ta na'ura batareda samun matsalaba(crash).

4.ya tabbatar da yasamar da daidai da BUQATAR abokin cinikini(client) Misali yace asamar masa da manhaja akan qa'ida da kuma lokaci

5.ya kasance mai bibiyar sabbin fasahohi dasuke bayyana da kuma sabbin kayan aiki(tools) da ake sabuntawa yau da kullum.

6.dole yakasace mai dabarun magana saboda aki ne na gamayya (team work).

7.yakasance mai lura sosai wajen tsarin tafiyarda manhaja (software life cycle).

ABIN LURA:
=>Software engineering aikine na gamayya(team) saboda yawanci manyan manhajoji mutun guda bazai iya kirkirar su a lokacin daya dace ba, dole sai an hada gamayyar injiniyoyi daga sassa daban daban misali kamar FACEBOOK,GOOGLE dake da almost layi miliyan dari, da billiyan biyu na code (100millionand 2billion line of code) bazai yiwu mutun guda yakirkira yakuma kula dashi ba dole sai an hada gamayya babba sannan a iya kirkira dakuma da tafiyar irin wadannan manyan manhajoji, wanda suna da yawa.


=> duk kanin abinda ake bukata agun software injiniya shine samar da ingantacciyar manhaja da kuma iya kulawa da ita wannan shine kashin bayan injiniyan manhaja.

=>gama rubuta manhaja baya nufin kagama da ita kula da ita yakan sa mutane dayawa acikin aiki mai dogon zango

=>wanda iya code yake rubutawa baida sauran ingancin da muka lissafa a sama su muke kira programer.

By:
(Nazeef mustapha fansheri)

@ASOF.2021
08038485677
Post a Comment (0)