*TAMBAYA TA 431*
*TA MUTU DA CIKI*
_Assalamu Alaikum._
Malam, idan mace ta rasu da ciki yaya za a yi? Za a binne ta haka nan ne, ko kuwa za a yi mata aiki a ciro jaririn ne?
*AMSA A431*
_W Alkm Slm W Rhmtul Laah._
Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:
كَسْرُ عَظْمِ الْمَيِّتِ كَكَسْرِعَظْمِ الْحَيِّ فِي الْإِثْمِ
Karya ƙashin mamaci kamar karya ƙashin rayayye ne a wurin zunubi. _(Abu-Daawud da Ibn Maajah suka riwaito shi, kuma a cikin littafin Irwaa'ul Ghaleel: 763 As-Shaikh Al-Albaaniy ya ce sahihi ne)._
Wannan, in ji malamai ya nuna Haram ne a karya ƙashi ko keta jikin mamaci don a cire wani abu sai in akwai wata larura mai ƙarfi. Kamar idan an buƙaci yin bincike a asibi domin gano musabbabin rasuwarsa. _(Tamaamul Minnah: 2/69)._
Don haka, idan an tabbatar da rayuwar jaririn a cikin marigayiyar, kuma ana kyautata zaton iya ceto shi a raye, to bai halatta a rufe ta da shi ba. Wajibi ne a ɗauki matakan yi mata aiki domin a fitar da shi.
Amma idan ba haka ba ne, kamar idan cikin bai yi girman da za a ce jaririn yana da rai ba, ko kuma ba a tabbatar yana da rai ba, ko kuma bai kai watanni haihuwarsa ba, ko kuma idan an tabbatar ko ana da marinjayin zaton cewa ko an fitar da shi ba zai rayu ba saboda ƙanƙantarsa da rashin na’urorin da za su iya taimaka masa wurin numfashi da sauransu, to a nan ba za a ce sai an yi matar aiki don ciro jaririn ba.
_Wal Laahu A’lam._
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
27/10/2020
3: 29pm.
*_Masjid Darul Qur'an_*