*ZAKKAR MAI BASHI:*
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
*TAMBAYA*❓
_As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah_ .
Manomin da 2/3 na kuɗin nomansa bashi ne ya ciwo, wai yaushe zai cire zakkah: Kafin ko bayan ya biya bashin ne?
*AMSA*👇
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .
(1) Al-Imaam Al-Baihaqiy ya ruwaito (7857) da irin isnadin Al-Bukhaariy (#7337) daga Sahabi As-Saa’ib Bn Yazeed _(Radiyal Laahu Anhu)_ cewa: Shi ya ji Uthmaan Bn Affaan _(Radiyal Laahu Anhu)_ yana huɗuba a kan mimbarin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ yana cewa: Wannan watan fitar da zakkarku ne. Sannan kuma ya ce:
فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ عَلَيْهِ دَيْنٌ فَلْيَقْضِ دِينَهُ ، حَتَّى تَخْلُصَ أَمْوَالَكُمْ ، فَتَؤَدُّوا مِنْهَا الزَّكَاةَ
Don haka, duk wanda akwai bashi a kansa to ya biya bashinsa, har sai dukiyoyinku su kuɓuta, to sai ku cire zakkar daga cikinsu.
Wannan ya nuna: A wurin Khalifah Uthmaan Bn Affaan da waɗanda suke tare da shi daga cikin Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ da Tabi’ai _(Rahimahumul Laah):_ Sai a bayan an cire bashi ne sannan ake cire zakkah.
(2) Sannan kuma Al-Imaam Al-Baihaqiy ya sake riwaitowa (7858) da ingantaccen isnadi daga Jaabir Bn Zaidin, daga Ibn Abbaas da Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhum)_ game da mutumin da ya ciwo bashi kuma ya kashe shi duk a kan gyara ’ya’yan itacen gonarsa da kuma iyalin gidansa. Shi ne Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya ce:
يَبْدَأُ بِمَا اسْتَقْرَضَ فَيَقْضِيهِ وَيُزَكِّى مَا بَقِىَ
Sai ya fara da bashin da ya ciwo ya biya shi, sannan ya fitar da zakkar abin da ya rage.
Watau dukkan bashin da ya kashe a kan gonar da iyalinsa.
Shi kuma Ibn Abbaas _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ cewa ya yi:
يَقْضِى مَا أَنْفَقَ عَلَى الثَّمَرَةِ ، ثُمَّ يُزَكِّى مَا بَقِىَ
Sai ya biya bashin da ya kashe a kan gonar, sannan ya fitar da zakkar sauran da ya ragu.
Watau ban da ɓangaren bashin da ya kashe a kan iyalinsa.
Amma idan ya kashe dukkan bashin a kan gonar ce har ma ya ƙaro kamar sulusi (1/3) daga aljihunsa, kamar yadda ya zo a cikin wannan tambayar, sai amsar ta zama:
Daga buhuna ɗari biyar (500) ko ɗari bakwai (700) da ya samu a gonar sai ya fara da ware adadin buhunan da farashinsu ya yi daidai da yawan bashin da ke kansa, sauran buhunan kuma sai ya raba su gida goma ya bayar da kashi ɗaya (1/10), idan da ruwan damina ne aka shayar masa da gonar. Ko kuma kashi ɗaya cikin ashirin (1/20), idan da ban-ruwa ne ya shayar da ita.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
_Wal Laahu A’lam._
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy