ZINA DA ƘANIN MIJI

*ZINA DA KAMIN MIJI* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Malam _na samu matsala ne a rayuwata ina zaune da mijina shekaranmu 7 da aure akwai kaninsa da yake bibiyata malam tun bana kulashi har ya kai yenzu har yakai muna wasa dashi._ 

 _Nayi nayi ya bari yaki bari. mai ya kamata inyi?_ 

 _Har ya saba inya shigo ya danneni har sai ya biya bukatansa akaina kuma bana iya che masa komai. Malam ataimaka mun da addu’oi da shawarwari._ 

 *AMSA* 👇


 _Hakika kin aikata kuskure babba. Domin kuwa bayan shirka babu wani zunubi mafi girma awajen Allah kamar zina._ 

 _Manzon Allah (saww) yace : “MAZINATA ANA HURA MUSU WUTA NE BISA FUSKOKINSU (RANAR ALKIYAMAH KENAN)._ 

 _( _Imam Tabaraniy ne ya ruwaito)._ 
 _Sannan acikin hadisai da dama Manzon Allah (saww) ya bayyana cewar Akwai wani ruwa mai bala’in doyi wanda ke fita ta farjojin Mazinata acikin Wuta. Wannan ruwan dashi ake yiwa sauran ‘yan Wuta Azaba.__ 

 _Sannan acikin wani Sahihin hadisi wanda Imamul Mundhiriy ya ruwaito acikin Targheeb wat-Tarheeb, Manzon Allah (saww) yace: “ALLAH YANA KUSANTOWA GA BAYINSA, SAI YAYI GAFARA GA DUK MAI NEMAN GAFARA. AMMA BANDA MATAR DAKE ZINA DA FARJINTA…. “._ 

 _Ya zama wajibi kiji tsoron Allah ki dena domin kuwa wannan laifin zai iya janyo miki bala’i da tozarta da wulakanta dake da danginki da iyayenki tun daga nan duniya. Aranar lahira kuma Farjin naki da kike zinar dashi, da kuma sauran gabobin jikinki sune zasu tona asirinki agaban Zatin Allah, ga dukkan halittu suna kallonki._ 

 _Zata yiwu ki samu ciki ta dalilin wannan Zinar, kuma ki shigo ma mijinki da wannan cikin (Ma’ana ba zai gane cewa cikin ba nasa bane). Alhali Manzon Allah (saww) yace:_ 

 _“DUK MATAR DA TA SHIGO MA WASU MUTANE DA WANI WANDA BA CIKINSU YAKE BA, TO ITA BA KOMAI BACE AWAJEN ALLAH. KUMA (ALLAH) BA ZAI SHIGAR DA ITA ALJANNARSA BA… “_ 

 _(Nisa’iy hadisi na 3481, Abu Dawud Hadisi na 2263)._ 

 _Shi kuwa wannan Qanin Mijin naki yaci amanar Allah da Manzonsa (saww), Kuma yaci amanar ‘Dan uwansa (wato mijinki). Kuma yana daga cikin mutanen da Allah yake yin tsinuwa agaresu._ 

 _Manzon Allah (saww) ya gaya ma Sahabbansa cewa “WALLAHI MUTUM YAYI ZINA DA MATAYE GUDA GOMA, SHI YAFI SAUKI AGARESHI (WATO SAUKIN AZABA AKANSA) FIYE DA YAYI ZINA DA MATAR MAKOBCINSA”._ 

 _(Imamu Ahmad da Tabaraniy ne suka ruwaitoshi)._ 

 _Acikin riwayar Ibnu Abid dunya kuma daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Umar (ra) : “WANDA YAYI ZINA DA HALAL DIN MAKOBCINSA (WATO MATAR MAKOBCIN KO KUYANGARSA) ALLAH BA ZAI DUBESHI BA ARANAR ALQIYAMAH (WATO BA ZAI MASA KALLON RAHAMA BA) KUMA BA ZAI TSARKAKESHI BA. KUMA ZAI CE MASA “SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGARTA)”._ 

 _To in dai haka lamarin yake akan matar Makobci, to yaya kuma matar ‘Dan uwa??_ 

 _Saboda guje ma faruwar irin wannan Fasadin shi yasa Manzon Allah (saww) yace : “KADA WANI MUTUM YA KEBANCE TARE DA WATA MACE, FACHE SAI TARE DA MUHARRAMINTA”._ 

 _Sai wani yace “Ya Rasulallahi shin Makusancin Miji fa?”._ 

 _Sai Manzo (saww) yace “MAKUSANCI AI SHINE MUTUWA” (Wato shine yafi ‘barna kenan)._ 
 _Abinda zakiyi shine :_ 

– _Da farko ki tuba zuwa ga Allah ki janye jiki daga wannan kwarton fasikin dake zuwa miki._ 

– _Ki hanashi shigowa amma idan bai hanu ba, Ki sanar ma mijinki cewa lallai ya hana wannan Qanin nasa shigowa inda kike._ 

– _Ki rika tuna lahirarki da kuma tsayuwarki agaban zatin Allah. Da kuma kusancin Allah gareki ako yaushe._ 

– _Ki sani cewa Biyan bukatar Sha’awar Minti biyar zata iya janyo miki Wulakantar duniya da lahira._ 

– _Ki tuna rayuwar yaranki da kuma tarbiyyarsu. Kuma ki dubi amanar Mijinki da kike ci._ 

 _Ki Yawaita Istighfari da Azumin nafilah domin samun tsarkaka daga wannan alfashar._ 

– _Idan Mijinki ba mazauni bane, gara ki matsa ki bishi wajen da yake aiki ku zauna achan domin samun tsira da Imaninki da mutuncinki._ 

– _Ki rika yin wannan addu’ar domin nisanta kanki daga alfasha : “ALLAHUMMA JANNIBNEE MUNKARATIL AKHLAQI WAL AF’ALI WAL AHWA’I”._ 

 _Allah ya sawwake ya gafarta miki ya shiryeki ya tsamoki daga kowanne laifi, tare damu baki daya._ 

Allah yasamu dace

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)