HUKUNCIN YIN AZUMI DA SALLAR DARE A WATAN RAJAB

*HUKUNCIN YIN AZUMI DA SALLAR DARE A WATAN RAJAB*

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf


                *TAMBAYA*❓

Salamu alaikum warahmatullah. Malam don Allah menene ingancin yin azumi a watan rajab? 
 
                           *AMSA:*👇

Wa alaikumus salam warahmatullah, to Dukkan Yabo ya tabbata ga Allah shi kadai. 

Da Farko: Shi watan rajab É—aya ne daga cikin watanni masu albarka wanda Allah ya ce:

“Lallai ne Æ™idayayyun watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne (a shekara) a cikin Littafin Allah, a Ranar da Ya halicci sammai da Æ™asa daga cikinsu akwai huÉ—u masu alfarma (na 1, 7, 11, 12 a cikin watanni). Wannan ne addini madaidaici. Saboda haka kada ku zalunci kanku a cikinsu. [Suratul Tawbah ayata 36].

Watannin masu alfarma su ne: Rajab, Dhu’l-Qa’dah, Dhu’l-Hijjah da Muharram.

Al- imamul Bukhari (4662) da imamul Muslim (1679) sun ruwaito daga Abu Bakrah (Allah ya Æ™ara masa yarda) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Shekara watanni huÉ—u ne da ita, wanda huÉ—u daga ciki masu alfarma ne: uku a jere, Dhu’l-Qa’dah, Dhu’l-Hijjah da Muharram, da Rajab Mudar wanda yazo tsakanin jumada da Sha'aban.

WaÉ—annan watannin ana kiransu da watanni masu alfarma saboda dalilai guda biyu:

1-Saboda an haramta yaki a cikinsu se dai idan maƙiyane suka kawo farmaki.

2-Saboda qetare iyaka acikin watannin masu alfarma shine mafi muni akan kowane lokaci.

Saboda haka Allah ya haramta mana aikata zunubai a cikin waÉ—annan watannin, kamar yadda ya faÉ—a: 
Saboda haka: “kada ku zalunci kanku a cikinsu.” [Suratul Tawbah ayata 36].

Ko da yake aikata zunubi haramun ne a waÉ—annan watannin dama wanda basu ba, amma a waÉ—annan watannin haramcin yafi karfi.

Al-Sa’di (Allah ya yi masa rahama) yace (p. 373): A cikin jumlar “kada ku zalunci kanku a cikinsu.” wakilin suna anan, za'a iya fahimtar cewa yana magana ne akan watanni sha biyu. Allah Ya ambaci cewa Ya sanya su su zama ma'auni na lokaci wa bayinsa, wanda zasu iya amfani dasu wajen bautamasa, kuma godiya ta tabbata ga Allah game da ni'imarsa.

Wakilin sunan zamu iya fahimtarsa a matsayin watanni huɗu masu alfarma yake nufi, kuma wannan ya haramtawa bayinsa saɓa masa a cikinsu, kamar yadda yake a koda yaushe haramun ne saɓawa Allah a ciki, saboda haramcin yafi karfi a wannan lokutan, amman yafi tsanani a wannan lokutan akan koda yaushe.

Abu na biyu: game da tambayarki akan yin azumi a watan Rajab, wannan kam babu wani sahihin hadisi da ya nuna cewa akwai wata lada ta daban a yin azumi duka ko wani shashe a watan Rajab.

Abinda wasu mutane suke yi, na azumtar wasu kwanaki a watan Rajab, da yin imani cewa su sunfi sauran mutane, wannan bashi da wani asali a cikin shari'a. 

Amma akwai ruwaya daga Manzon Allah (SAW) wanda ya nuna cewa Mustahabbi ne yin azumi a watannin nan masu alfarma (kuma Rajab yana daga cikin watannin masu alfarma). Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku azumci wasu kwanaki daga watanni masu alfarma amma banda sauran watanni.” Abu Dawood ya ruwaito shi, a hadisi me lamba ta 2428; amma hadisin Albani ya da'ifanta shi a cikin Da’eef Abi Dawood.

To amma koda wannan hadisin sahih ne wato ya sha, to yana nuna mana cewa mustahabbi ne yin azumi a watanni masu alfarma. Saboda haka idan mutum yayi azumi lokacin Rajab saboda wannan, kuma sannan yayi azumi a wasu watannin masu alfarma, to babu komai akan hakan. Amman ware Rajab shi kadai da cewa za'ayi azumi a ciki wannan kuskure ne ba dai dai ba ne!

Shaikhul Islam Ibn Taymiyah (Allah yayi masa rahama) ya ce acikin Majmoo’ Fataawa (25/290): 

Ga me da yin azumi a watan Rajab kadai, to hadisan da suke magana akan hakan duk basu inganta ba, ballama hadisai ne wanÉ—anda suke kirkirarru (wato na Æ™arya). Malamai basu dogara da ko É—aya daga ciki ba. Basa ma daga cikin da'ifan hadisai waÉ—anda aka ruwaito su, se dai ma mafi yawansu kirkirarrun hadisai ne da karya. Acikin al-Musnad da wasu guraren akwai hadisai da suke cewa Manzon Allah (SAW) yana son yin azuni a watanni masu alfarma, wanda sune Rajab, Dhu’l-Qa’dah, Dhu’l-Hijjah da Muharram, amma wannan yana da alaqa ne da yin azumi a dukkansu, ba iya rajab ba kawai.

Malam Ibn al-Qayyim (Allah ya yi masa rahama) yace: Duk wani hadisi wanda ya ambaci yin azumi a Rajab da yin salla a wasu dararensa wannan Æ™arya ne kuma Æ™irkirarran abu ne.” Duba al-Manaar al-Muneef, shafi. 96

Al-Hafiz ibn Hajar yace a cikin Tabyeen al-‘Ajab (shafi na. 11):

Babu wani sahihin hadisi da za'a iya ƙirgawa wanda yayi magana akan nagartar watan Rajab, ko wani shashe nasa, ko bata wani dare nasa da salla.

Shaykh Sayyid Saabiq (Allah ya yi masa rahama) ya ce acikin Fiqh al-Sunnah (1/282):

Yin Azumi a Rajab be fi yin azumi a wasu watannin ba, se dai cewa yana daga cikin watanni masu alfarma da falala. Babu wata sahihiyar ruwaya a sunna da ta dauka cewa akwai wata falala ta daban a yin azumi a wannan watan. Duk abinda aka ruwaito game da hakan to be inganta da shi ba a matsayin hujja.

Shaykh Ibn ‘Uthaymen (Allah yayi masa rahama) an tambaye shi game da yin azumi a 27 ga watan Rajab da tsayuwar dare a darenta. Sai yace: 

Yin Azumi a 27 ga watan Rajab da tsayuwar darenta da salla bidi'a ne kuma ko wace bidi'a É“ata ce.

Majmoo’ Fataawa na Ibn ‘Uthaymeen, 20/440.

Kuma Allah ne mafi sani.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)