*MAKARANTAR AZUMI 009* //
📌 ```ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI```
Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mai Azumi ya nesance su, domin idan ya aikata su da Rana tsaka a Ramadana, sai Azumin sa ya ɓaci, zunuban sa su yawaita, Malamai sun gano cewa waɗannan abubuwa masu ɓata Azumi, za’a iya kasa su karkasuwa mai yawa, dangane da ire-iren sakamakon da ake haifarwa daga gare su kamar haka:
Na farko: *CI DA SHA DA* *GANGAN* ; wannan yana bata Azumi abisa haduwar Malami
Na biyu: *ƘAƘARO AMAI* *DA GANGAN* ; duk wanda ya fitar da wani abu daga cikin shi to Azumin shi ya baci, amma duk kuwa wanda amai ya rinjaye shi to babu komai akanshi, kuma Azumin shi yayi –in Allah yaso- dalili akan haka faɗar Manzon Allah: “Duk wanda Amai ya kuɓuce masa – alhali kuma yana Azumi – wannan babu ramuwa akanshi, amma idan ya ƙaƙaro shi da gangan to sai ya rama Azumi” [Abu Dawuda ya ruwaito shi daga Abu Hurairah]
Na uku: *HAILA DA* NIFASI; idan Mace tayi Haila ko tayi Nifasi (Jinin Haihuwa) a wani yanki na wuni a farkon wuni ne ko a karshen sa to anan sai taci abincin ta, sai ta rama azumin ta daga baya, idan kuwa ta cigaba da Azumi to azumin ta bai yi ba.
Na Hudu: *JIMA”I;* Malamai sun haɗu akan cewa kai-tsaye yana ɓata Azumi, saboda Hadisin da Bukhaariy da Muslim suka fitar dashi daga Abu Hurairah.
✍ *ANNASIHA TV*