CIYAR DA MAI AZUMI


*MAKARANTAR AZUMI 008//*

📌 _CIYAR DA MAI AZUMI_ 

Kayi ƙoƙari ya ɗan’uwa Allah ya albarkace ka, kuma yayi maka gamo-da-katar ga aikata alheri, da bin dokokin Sa wajen shayar da mai Azumi koda ruwa ne, akwai mabuƙata da yawa, wasu basu da abunda zasu saka a baki idan sun kai Azumi, waɗanda suke dashi ɗin ma bai taka kara ya karya ba, dashi suke buda-baki abunda yayi saura suyi Sahur dashi, kaji tsoron Allah dan’uwa kada ka tara kayan cin dadi, alhali ga makwabcin ka yakai Azumi, amma yanata mazurai saboda ya rasa abunda zai saka a cikin sa, yin hakan akwai lada mara misaltuwa da Bawa zai samu a wajen Ubangijin sa na ciyar da mai Azumi da yayi. Kamar yadda yazo a Hadisin da aka karbo daga Zaid ɗan Khalid (RA) yace: Manzon Allah ﷺ yace: “ *Duk wanda ya ciyar da mai Azumi zai kasance yana da Lada irin ladan mai Azumin* , *sai dai kuma babu abunda zai rage na Ladan shi mai Azumin* ”. [Tirmizhiy ne ya riwaito shi]
 

 *HANI AKAN YIN SAƁI ZARCE* 

Azumin saɓi zarce shine mutum bayan Rana ta fadi bazai ajiye Azumi ba sai ya wuce da Azumin sa sai washegari yasha ruwa, wato Azumin kwana biyu a haɗe, mafi yawancin Malamai sun tafi akan haramcin yin haka, sai dai kaɗai ya kebanta ne ga Manzon Allah (SAW) shi kaɗai, dalilin su akan haka abunda Bukhaariy da Muslim suka ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar (RA) ya ce: Lallai Manzon Allah ﷺ yayi hani da yin sabi zarce a Azumi sai Sahabbai suka ce to Ya Manzon Allah ai kai kana yin sabi zarcen, sai Yace musu: “ai ba kamar ku nake ba domin Allah ne yake ciyar dani kuma yake shayar dani”.

✍ *ANNASIHA TV*

*Twitter* 👇
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09

*Telegram* 👇
https://t.me/AnnasihaTvChannel
Post a Comment (0)