AN SANYA MINI RANAR AURE, WADANNE ABUBUWA YA KAMATA NA KIYAYE?
https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum,
Dafatan mlm yatashi lpy,
Mal nice aka sanya mini rana ankawo kudin sadaki amma lokacin bikin zai kai nanda watanni bakwai,
Dame dame yakamata inkiyaye amatsina na wacce akasanya mata rana wurin mu'amala da sauran jama'ah da samari.
Nagode mall
*AMSA*👇
Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in
Farko dai ki zamo mai taqwa, tsoron Allah da kiyaye dokokin Sa
99 - «اتق الله يا أبا الوليد لا تأتي يوم القيامة ببعير تحمله وله رغاء أو بقرة لها خوار أو شاة لها ثؤاج»
(صحيح) ... [طب] عن عبادة بن الصامت. الصحيحة 857: هق.
Ki sassauta ganin ki a kan sauran maza, ki kiyaye bayyanar da adon ki ga kowa sai muharramin ki, sannan ki lazimci hijabi da nikabi, ta yadda galibin maza ba zasu ga fuskar ki ba, ballantana su yi sha'awar zance da ke ko kuma wata magana ta taso.
(وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَـٰتِ یَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَـٰرِهِنَّ وَیَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا یُبۡدِینَ زِینَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡیَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُیُوبِهِنَّۖ ...)
[Surah An-Nur 31]
Idan kuma wani yayi maki magana kice da shi, inni swa'imun
(.... فَإِمَّا تَرَیِنَّ مِنَ ٱلۡبَشَرِ أَحَدࣰا فَقُولِیۤ إِنِّی نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَـٰنِ صَوۡمࣰا فَلَنۡ أُكَلِّمَ ٱلۡیَوۡمَ إِنسِیࣰّا)
[Surah Maryam 26]
Ki kula da addini, ba kamar sallah a lokacin ta.
(ٱتۡلُ مَاۤ أُوحِیَ إِلَیۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَـٰبِ وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَۖ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَاۤءِ وَٱلۡمُنكَرِۗ وَلَذِكۡرُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۗ وَٱللَّهُ یَعۡلَمُ مَا تَصۡنَعُونَ)
[Surah Al-Ankabut 45]
Ki nisanci ziyartar Mallaman tsubbu da sunan zasu yi maki istihara ko su baki dafa'i ko bita zaizai don ya kara son ki, hakan shirka ne, kafirci ne.
عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما عن النبي - صلى الله عليه وسلم - قال:
"من أتى كاهنا فصدقه بما قال؛ فقد كفر بما أنزل على محمد - صلى الله عليه وسلم -".
Ki mayar da hankali wajen koyon addini musamman abinda ya shafi hukuncin aure, takaba, saki, idda, tsarki, zihari, khul'i, li'ani da sauran darusa da suke da alaka da aure. Hukuncin ciki, haihuwa, shayarwa, yaye, raino da tarbiya. Ki kara da neman matsayar musulunci dangane da halasci ko haramcin tsarin iyali, kaiyade shi da amfani da abinda ke da alaka da hakan.
Ki dauki lokaci wajen kara koyo da kwarewa wajen iya girki, ya zamo ke zaki dinga girki a gidan ku ba mahaifiyar ki ba ko kannen ki ba.
Ki yi hakuri, ki wadatu da abinda Allah ya baki a yanzu, domin shaidan ba zai gushe ba, yana angazo ko hankado maki maza, yaran su da manya, tare da kawata maki su a ido da zuci, har idan baki kai zuciya nesa ba, kice kin samu wanda ya fi shi, kin fasa.
6027 - «من استغنى أغناه الله ومن استعف أعفه الله ومن استكفى كفاه الله ومن سأل وله قيمة أوقية فقد ألحف» .
(صحيح) [حم ن الضياء] عن أبي سعيد. الصحيحة 2314.
Ki kara kamewa daga duk nau'in wani zance da sauran duk wani ajanabi, ta wayar sadarwa ko kuma kowace hanya. Tun yanzu ya zamo wajibi ki ladabtar da kan yin hakuri da namiji daya tal wajen kowace mu'amala da shara'a ta baki. Yanzu zamani ne da ha'inci na da sauki, amma kuma bincike da kama maha'inci na da sauki, ta hanyar wannan wayar ta sadarwa.
Yana da kyau ki daina yawo maras dalili da zuwa biki ko kwana a gidan biki. Ki tace kawaye tun yanzu da kuma ajiye sirrin ki a kirji. Ki mayar da iyayen ki, abokanan tattauna matsalar ki da neman shawara.
Ki ci gaba da yin istikhara har ki samu natsuwa da wannan bawan Allah da zai aure ki. Sannan idan kina da wani saurayi ko lambar shi, ki tsoraci Allah ki share wayar ki, kamar wacce aka yiwa welcome back, bayan nan duk wanda ya bugo, da kin gane muryar shi, ki yi reject da block din shi, babu dogon zance, idan yayi sms, kar ki bashi amsa.
Daga karshe, sai ki yawaita addu'a, Allah ya taimake ki, tare da lazimtar azkar na safe da yammaci. Ina ganin insha Allahu, haka ma ya wadatar idan har zaki iya. Allah ya kai mu lokacin muna da rai da lafiya, yasa ayi da mu, yayi maku albarka, ya tara tsakanin ku cikin alkhairi aamin.
Wallahu ta'ala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*