MAGANIN RAGE YAWAN SHA'AWA



MAGANIN RAGE YAWAN SHA'AWA:

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu Alaikum.ni Allah ya jarafceni da karfin sha'awa kuma banda halin yin aure shine nike neman ataimaka man a fada mani magungunan rage sha,awa domin gudun fadawa ga halaka.nagode a huta lafiya.

 *AMSA* 👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Daga cikin abubuwan dake rage yawan motsawar sha'awa ajikin Dan Adam, akwai :
- Kiyaye dokokin Allah ta fuskar runtse idanuwanka daga kallon haram, ko karanta haramtattun abubuwa. Ko kuma furta haramtattun kalamai (Na batsa).
- Yawaita yin azumi da nafilfil da kuma mayar da hankali akan abinda ya shafi lahira. Musmman mutuwa, Kwanciyar Qabari, da sauransu.
- Yawaita shan Lemon tsami (Idan baka da Olsa). Ko kuma Jar kanwa ('Yar Qalilan).
- SHAJARATU MARYAM : Bishiya ce wacce ake amfani da ita don magance matsalolin Mata.
Amma Idan namiji yasha, tana cire masa sha'awa sosai daga jikinsa da zuciyarsa. Da ita ne Mutanen da chan, irin masu yawan ibadan nan suke amfani domin samar ma kansu cikakken hutu daga wannan.

WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)