BAYYANA KARATU GA MATA



BAYYANA KARATU GA MATA 

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum.

Menene ingancin bayyana karatun sallah ga mu mata?

*AMSA*👇

W Alkm Slm W Rhmtul Laah.

Malamai sun yi ijma’i a kan bayyana karatu a cikin dukkan raka’o’i biyu na sallar Asubah, da raka’o’i guda biyu na farkon sallar Maghriba, da raka’o’i guda biyu na farkon sallar Isha’ai. Haka kuma da sirranta karatun a cikin dukkan raka’o’in sallar Azahar da La’asar da raka’ar karshe ta Maghrib da raka’o’i biyu na karshen Isha’i. (Aslus Sifah: 2/413)

Sannan kuma ya tabbata a cikin Hadisin Maalik Bn Al-Huwairith (Radiyal Laahu Anhu) cewa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« وَصَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِى أُصَلِّى »
Kuma ku yi sallah kamar yadda kuka ganni ina yin sallar. (Sahih Al-Bukhaariy: 631)

Wannan gamammiyar dokar ta hade maza da mata daga cikin musulmi, sai in an samu wurin da ya cire matan daga hakan. 

Al-Imaam Al-Mujaddid Al-Albaaniy a ƙarshen littafinsa: Sifatu Salaatin Nabiy (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayyana cewa: 

Babu wani abin da ya zo a cikin Sunnah da yake hukunta cire mata a cikin siffar Sallar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Har kuma ya kawo maganar da Ibn Abi-shaibah ya riwaito da ingantaccen isnadi daga Ibraahim An-Nakha’iy (Rahimahul Laah) ya ce:

تَفْعَلُ الْمَرْأَةُ فِي الصَّلَاةُ كَمَا يَفْعَلُ الرَّجُلُ
Mace a cikin sallah tana aikata irin abin da namiji yake aikatawa ne. (Aslus-Sifah: 3/1040) 

Sannan kuma yana da kyau mu san cewa: Bayyana karatu ba yana nufin daga murya sai kowa da kowa a kusa da na nesa ya ji ba ne. Amma dai ɗagawa ne ta yadda mai sallah zai jiyar da kansa da wanda yake kusa da shi.

Kuma maganar cewa wai muryar mace al’aura ce ba daidai ba ce, domin dai maganar Allaah Ta’aala ta warware ta inda yake cewa:
 یَـٰنِسَاۤءَ ٱلنَّبِیِّ لَسۡتُنَّ كَأَحَدࣲ مِّنَ ٱلنِّسَاۤءِ إِنِ ٱتَّقَیۡتُنَّۚ فَلَا تَخۡضَعۡنَ بِٱلۡقَوۡلِ فَیَطۡمَعَ ٱلَّذِی فِی قَلۡبِهِۦ مَرَضࣱ وَقُلۡنَ قَوۡلࣰا مَّعۡرُوفࣰا
Kuma ku faɗi magana kyakkyawa ta alheri. (Surah Al-Ahzaab: 32)

Wace magana ce kuwa ta fi Alqur’ani kyau da alheri?!

Allaah ya fahimtar da mu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Asslafiy

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)