*FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN*
=
=
*DAGA ZAURAN*
=
*TARBIYYATUL AULAD*
=
*What'sApp*
```08168315013```
```08162332323```
=
*=18/9/1441*
*11/5/2020*
*FITOWA TA TALATIN DA SHIDDA*
.Cigaban Karatun littafin
_FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN_ _Akan koyarwar Alqur'ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na kwarai._
*LITTAFI NA DAYA*
*NA*
```SHEIKH ABDULWAHAB ABDALLAH```
=
=
*TAMBAYA TA 57*
```Mene ne matsayin zakkar fidda-kai (Zakatul fidri)?```
*AMSA :*
Zakkar fidda-kai sunnah ce daga cikin sunnunin Manzon Allah tsirada amincin Allah suqara tabbata agareshi Hakika Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya fitar da zakkar fidda-kai,kuma sahabbansa masu albarka sun aikata hakan. Domin hadisi ya tabbata daga Abu sa'idinal khudri Allah ya qara masa yarda yace :mun kasanci muna bayar da ita a zamanin Annabi sallallahu alaihi wasallam sa'i daya daga abinci ko sa'i daya daga dabbino, ko sa'i daya daga alkama, ko sa'i daya daga zabibi (wato busheshshen inibi)
Awata ruwayar kuma
Sa'i daya daga cikwi.
Za'a iya fitar da wannan Zakkar kafin ganin watan shawwal da kwana biyar zuwa goma, domin sahabbai sun aikata haka.Haka kuma ana fitar da zakkar ga kowanni musulmi,yaro da Babba mace da na miji,da (mai 'yanci)da bawa.kuma ana fitar wa kuwanne mutum mudannnabi hudu.Amma abin mamaki wasu mutanen ba su damu da fitar da ita ba, saboda aganinsu su kansu talakawa ne daya kamata abawa zakkar. Bayan kuwa wasu malaman sunce lallai mutum zai fitar da zakkar fudda Kai, guda kuwa rigarsa biyu ce, sai ya sayar da daya domin ya fitar da ita.
_Zamu dakata anan sai lokaci na gaba da yardar Allah_
=
=
✍🏻. *RUBUTAWA*
```RUQAYYA AUWAL USMAN```
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka Wanatubu ilaika
