*IDAN AN GAMA AZUMI SAI KUMA ME?*
π Sai a yi farin ciki. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce: " Mai azumi yana da farin ciki biyu; farin ciki yayin buda bakinsa...". Muslim.
π Su ne:
* Karamin farin ciki: Kullum bayan Magariba.
* Babban farin ciki: ranar Idi
♦ Farin Ciki cewa Azumi Ya kare iri biyu ne:
* Mai Takawa: Yana farin cikin yi wa Allah biyayya, Yana farin ciki da hakan.
* Mai Sakaci: Yana murna an daina kishirwa da yunwa, da tashin dare, Yana farin ciki ba zai ci gaba ba.
π» Farin Ciki da Idi
* Ibada ne
* alama ce Mai bayyana Musulunci
* Wanda ya ce a yi murna da azumi shi ya ce a yi murna da Idi
π»Saboda me za ka yi Farin Ciki da Idi?
π Don Ka amsa Kira zuwa walimar Allah
* Za ka yi farin ciki kai kanka
* Ka faranta wa waninka
* Waninka ma ya faranta maka.
* Gaba dayanku Allah Ya faranta muku.
π Farin Ciki Da Idi Zai kasance ne:
* Da Zuciya
* Da Zantuka
* Da aiki
* Da Dukiya
π» Farin Cikinka da Idi Ba shi da Alaka da Wadatarka, ko Yanayin da Zuciyarka.ke ciki, ko Halinka a cikin Al'umma:
*Idan hankalinka a kwance yake, ka kara farin ciki Sai kwanciyar hankalinka ya karu
* Idan kana cikin damuwa, ka yi farin ciki Sai damuwarka ta gushe
* Idan kana cikin wadata, yi farin ciki ba zai salwantar da dukiyarka ba
* Idan kana cikin kuncin rayuwa, yi farin ciki domin ibada kake yi.
# Idan kana cikin ibada, yi farin ciki domin Karin ibada ne da Allah ya azurta ka da ita
# Idan kai mai sabo ne, ka yi farin Ciki da Idi, Sai ya ba ka halal da za ka wadatu daga aikata haram.
π» Farin Cikinka Ranar Idi:
*_* Zai faranta wa bayin Allah na gari
*^* Zai bakanta wa makiya Allah
πΈBarkanmu da Salla malamai!
πΈAllah Ya maimaita Mana malamai!!
πΈAllah kara maimaita Mana malamai!!!
Taqabbalallahu minna wa minkum
Kullu aam wa antum bi khair.
*Dr.* *Abdulkadir Ismail*
