KUJE KU KOYI ILIMIN AURE KAFIN KUYI AURE👩❤️👨
_(Wannan sakon yanada muhimmanci ga duk wanda ya faɗa a wayarsa ya karanta, kuma ya yadata don a samu a taimaka ilimi ya bunkasa)._
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 26/ 11/ 1441 wanda yayi dai-dai da 17/ 07/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._
_Bayan haka, jama'a wannan takaitaccen bayani ne ko kuma ince shawarwari ne da zan bayar ga masu neman aure. Domin ganin yadda za a magance rigimgimu da matsaloli akan aure da kuma karin aure. Babu shakka ana samu matsaloli da dama wanda mafi yawan wannan matsalolin rashin ilimin auren ne yake jawowa, musamman mazan mu na yanzu da basuda wannan ilimin, domin idan namiji yanada ilimin zamantakewar aure tho za a samu zaman lafiya, amma idan mace ce take da ilimin zamantakewar aure, alhalin shi namijin bashi da ilimin, tho fah babu zaman lafiya, domin shi namijin shine jagora. Amma samun cikakken zaman lafiya kuwa shine duk ku kasance masu ilimin zamantakewa. Ina fatar an fahimta??_
_Inaso wannan lekcar ku yadata yadda za a samu mutanen da za a hadu a taimaka ilimi ta bunkasa ta fannoni dayawa, a kafa makarantu na certificate, yadda duk wanda yake da niyyar yin aure, tho sai yaje wannan makarantar an koyar dashi ilimin zamantakewar aure, idan ya kammala karatun, tho sai a bashi certificate na tabbatar da cewa yanada ilimin zamantakewar aure. Hakama yar uwa kema sai kinje kin karanci ilimin zamantakewar aure, yadda idan kin kammala za a baki certificate na tabbatar da cewa kinada ilimin zamantakewar aure. Na rantse da Allah ina mai tabbatar muku cewa idan akayi haka, tho shikenan an kawo karshen rigimgimu da matsaloli a zamantakewar aure, saboda dukkaninsu sunsan hakkokin dake kansu, kuma dukkaninsu sun samu ilimin hakuri da juna. Tho kunga kenan an kashe hanyoyin da za a dinga samun matsaloli kenan ko? Wannan shawara ce na bayar kyauta, saboda haka wadanda suke da hali su dubi wannan da kyau, ku bada gudummawa ilimi ya bunkasa a kasar nan tamu ta Nigeria. Ya zama duk sadda kaje neman aure, tho bayan an tabbatar halayyarka Masha Allah, tho abu nagaba shine ina certificate dinka? Idan bakada certificate, tho shikenan sai kaje ka koya kuma ka iya sannan za a baka, wallahi tuni za a magance wadannan matsalolim da ake samu a zamantakewar yanzu._
_Tsakani da Allah kai me karatu da zakayi aure kasan hikimomin yin auren? Kasan hakkokin dake kanka kafin kayi auren? Kasan abinda shari'a ta tanadar ga masu aure? Hakama yar uwa kema kinsani?_
_Tho bakusani ba amma kuka sa rai za a samu zaman lafiya? Jama'a zaman lafiya bazai yiwu ba idan ba a san hakkokin juna ba, dolene ya zamana kunada ilimin zamantakewar aure, tho anan ne za ayi rayuwar aminci da soyayya. Saboda haka ina bada shawara ga gwamnati da masu hali da wadanda suke da rufin asiri su hadu su taimaka su bunkasa ilimin zamantakewar aure, su taimaka su bada gudummawa a kafa makarantaku, a kafa kungiyoyi a online wanda za a dinga karantar da yan uwanmu maza da mata wannan ilimin ta zamantakewar aure, a kafa kungiyoyin mata daban, kungiyoyin maza daban a kafafen sadarwa da makarantu. Jama'a mu taimaka mu raya sunnar Manzon Allah s.a.w, mai bada filin ginin makaranta ya bayar, mai siyan blow ya siya, mai bada kudi ya bayar, duk a hadu a taimakawa jama'a a fidda su daga jahilci zuwa haske, wannan aikin shima yana daga cikin *SADAKATUL JARIYAH* wato sadaka mai gudana. Ku tuna fah akwai lokacin da zai zo wanda zaka tsinci kanka/ki a kabari, wanda a wannan lokacin dukkanin ayyukanka sun yanke sai aikin da kayi me gudanarwa wato *SADAKATUL JARIYAH*. Tho saboda haka mu hadu mu raya sunnar Manzon Allah s.a.w mu yaki jahilci, domin zaman jahilci wasu sukeyi a zamantakewa. Gwamnati taji wannan da kyau, tunda gwamnati tana iya bada gudummawa wajan gina gidajen kallo da gidajen wasa, tho muna kira ga gwamnati Dan Allah ta gina mana makarantu, ta bunkasa ilimi._
_Jama'a wasun mu na wasa da addininmu basu dauki addini da muhimmanci ba kamar yadda suka dauki neman duniya da muhimmanci. Duk sadda mutum zai siya mota tho sai yaje ya fara koya tukun sannan zai siya, ko kuma ya siya din ya ba wani ya koyamasa. Hakama duk sadda zaka fara business, tho sai kaje gurin wadanda suka san harkar su koya maka sannan zaka fara business din. Amma saboda ba a dauki addini da muhimmanci ba duk sadda mutum ya tashi neman aure, tho bazai je ya koyi ilimin zamantakewar aure ba, kawai indai yana da abin duniya shikenan ba abinda ya dameshi, ko ba haka bane? Shiyasa zakaga matanmu sun nace lallai-lallai sai mai kudi sai mai mota. Tsakani da Allah inda ace sunada ilimin zamantakewar auren zasu fadi haka? Amma na rantse da Allah inda sunada ilimin zamantakewar aure, tho wallahi ko mijin bashida ko sisi, sai ta yadda ta aureshi indai yanada hali me kyau, domin tasan irin daraja da lada mai yawan da zata dinga samu. Amma rashin ilimin ne yasa suka nace lallai-lallai sai mai kudi. Acikin 'ya'yan masu kudi kashi 85% acikinsu bazasu iya auri wadanda basuda babban gida da mota ba, saboda ta saba shiga mota, nan da nan idan zata a gidansu, tho da mota ake kayita, tho yaushe zaka aureta bakada machine? Yarinya ta saba da cin abu mai dadi iri-iri, kai kuma ka saba cin taliya me man gyada, tho wane zaman lafiya zaka samu da ita? Amma inda ace sunada ilimin zamantakewar aure, tho bazasu dubi abun duniya ba, falalar dake cikin zamantakewar auren zasu duba._
_Jama'a akwai bukatuwar a taimaka ilimi ya bunkasa a kasar nan tamu, abin mamaki zaka samu mace ta kware wajan iya soyayya da iya romantic love, amma idan ka aureta, tho sai ka nemi wannan romantic din ka rasa. Nasan yanzu mata zasu fara cewa ai maza ne suke haka ko? Tho kusani shi namiji idan yana son abu, tho duk hanyar da zai bi yaga ya samu wannan abin tho zaiyi, saboda haka kada kuyi mamaki idan kin rasa soyayyar da yake nuna miki kafin aure domin haka wasu mazan suke, zasuyi ta nuna miki soyayya amma da zarar anyi auren sai a nemi soyayar a rasa. Kuma abin takaici idan yaci sa'a ya samu mace wacce ta iya romantic love sai ya dinga wani kaf-kaf da kai kamar gaja ko wawa, shi gashi bai iya romantic love ba, amma ya samu wacce ta iya romantic love, amma baya jindadi. Kunga wannan matsala ne babba. Saboda haka jama'a kuje ku nemi ilimi. Kuna ganin yadda arna suke rayuwar su ta zamantakewar aure, idan mijin zai tafi office, tho matarsa sai ta rakashi bakin gate sannan ya sumbaceta kafin ya tafi, amma kai gaja ka kasa, amma sadda baka aureta ba ka cika ta maganganun karya da munafunci._
_Saboda haka Dan Allah jama'a mu taimaka mu raya sunnar Manzon Allah s.a.w, mu kafa makarantu mu kafa kungiyoyi a kafafen sadarwa. Allah Ubangiji yasa wannan sakon ya isa gun wadanda suke da ikon taimakawa jama'a, wadanda suke da ikon kafa makarantu da kafa kungiyoyin da za a dinga karantar da yan uwanmu a online. Allah Ubangiji ya taimake mu, ya bamu ikon taimakawa yayi mana albarka, yasa mudace._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
*_(ABU-MANAL)_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.